Kungiyar ECOWAS na son a biya diyyar corona
March 8, 2021A ci gaba da kokari na janyo hankulan ‘yan Najeriya don su rungumi shirin yin allurar rigakafin cutar corona da aka fara a kasar, Kungiyar gamayyara Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) ta bukaci kasashen su biya diyyaga duk wanda ya fuskanci wata matsala sakamakon allurar corona. Ko wane tasiri wannan zai yi a kokari na samun karbuwar allurar da kawar da rashin yarda a zukattan wasu daga cikin al'ummar kasa? Wannan ita ce tambayar da jama'ar kasar ke son sanin amsarta. Karin Bayani: Agajin riga-kafin corona ga Afirka
Kwanaki uku da fara allurar rigakafin cutar ta Covid 19 a Najeriyar ne, Kungiyar Ecowas ta bullo da batu na samar da kyakyawan tsari don biyan diyya ga duk wanda ya samu wata matsala sakamakon allurar rigakafin cutar ta Covid 19 a kasashen Afrika ta yamma, sanin cewa Najeriyar ta bi sahun kasar Ghanawajen samu dama fara aiwatar da allurar da ake cike da fata za ta taimaka murkushe wannan annoba da ta girgiza duniya. Tuni dai jami’an kula da lafiya da kungiyoyi kare hakin jama’a ke bayyana ra'yoyi kan tasirin da wannan zai yi wajen kara cusa yarda da ma tabbatar da kare hakkin duk wanda ya karbi allurar.
Sanin cewa har yanzu kasashen Afrikan sun dogara ne a kan samar masu da allurar cutar ta Covid 19 abin da ke sanya daga 'yar yatsa. Ministan Lafiya a Najeriyar Dr Osagie Ehanire ya bayyana matakan da aka samar domin tabbatar da babu batu na jabun alluran rigkafin a Najeriya yana mai cewa. ‘’Ya ce duk wata allurar rigakafin da bata samu amincewar hukuma kula da inganci abinci da magunguna ta Najeriya ba, to an dauketa tana da hatsari kuma jami’an hukumar da na kwastom za su sa ido, tuni akwai allurarar corona na jabu a kasuwanin duniya, gwamnatin Najeriya a shirye take da biyan dukkanin bukatu a wannan fani'' Bullo da biyan diyya ga wadanda allurar ta corona za ta yi wa illa dai babban mataki ne da zai kawar da yanayi na dar-dar da ake fama a sassan Najeriyar.