1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

EU ta cimma matsaya kan 'yan gudun hijira

Abdullahi Tanko Bala
October 4, 2023

Sanarwar cimma yarjejeniyar ta zo ne bayan da kasashen Italiya da Jamus suka warware sabanin da ke tsakaninsu kan kungiyoyin agaji da ke ceto 'yan gudun hijira da suke watangaririya a kan teku

https://p.dw.com/p/4X6oD
Ceton 'yan gudun hijira a kan teku
Ceton 'yan gudun hijira a kan tekuHoto: Pau de la Calle/AP/picture alliance

Kasashen na EU dai sun bukaci sabunta manufofin ne yadda za su tunkari matsalar 'yan gudun hijirar idan aka sami kwarar masu neman mafaka zuwa cikin tarayyar Turai.

A wannan makon shugabannin kasashen Turan za su hallara a birnin Granada da ke kudancin kasar Spain domin tattauna batun bakin hauren.

Shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta jinjinawa yarjejeniyar da za ta sauya lamura.