1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hezbollah da Isra'ila na gwabzawa a kan iyakarsu

Abdourahamane Hassane
October 20, 2023

Fada na kara rincabewa a kan yankin iyaka tsakanin Israi'ila da mayakan Hezbollah na Lebanon masu goyon bayan Hamas.

https://p.dw.com/p/4XpnD
Hoto: JALAA MAREY/AFP

Sasan biyu na ta yi barin wuta da makaman atilare tun lokacin daHamas ta kaddamar  da hari a ranar 7ga watan Oktoba a kan Isra'ilar ma'aikatar tsaron Isra'ila ta sanar da cewar za ta kwashe jama'ar dake a garin  Kyriat Shmona, wanda yawanci mazauna garin dubu 25,000 wasun su har sun riga sun arce. Kasashen duniya na fargabar barkewar rikici tsakanin kungiyar  Hezbollah ta Lebanon mai goyon bayan Iran,da Hamas da kuma sojojin Isra'ila. kusan mako guda kenan da sojojin Isra'ila ke cikin shirin ko-ta-kwana a kan iyakarsu da ke arewacin kasar Lebanon domin tunkarar harin daHezbollahka iya kai wa.