Fafaroma ya koka da kisan manoma a Najeriya
December 2, 2020Talla
Fafaroma Francis wanda ya kwatanta kisan manoman da ake zargin mayakan Boko Haram da aikatawa da kisan kiyashi irin na ta'addanci, ya kuma wannan wani abu ne da yake matsayin babban laifi.
A jawabin da ya yi a fadarsa ta Vatican, ya yi alkawarin yi wa Najeriya addu'o'i, kasar da ke fama da rikice-rikice da ke haddasa matukar asarar rayuka.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiyar da ta dauki alhakin harin wanda aka dora kan mayakan tarzomar Boko Haram.