1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Frashin shinkafa ya haura a duniya

Abdourahamane Hassane
September 8, 2023

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya FAO ta ce farashin shinkafa a duniya ya kai matsayinsa mafi girma cikin shekaru 15 a cikin watan Agusta, inda ya karu da kashi tara da diko takwas cikin dari.

https://p.dw.com/p/4W7a6
Afrika Ghana Accra Markt
Hoto: OLIVIER ASSELIN/AP/picture alliance

Hakan ya biyo bayan da Indiyata hana fitar da farar shinkafar basmati, kimanin kashi ɗaya bisa huɗu na shinkafar da aka saba fitarwa saboda tanadin al ummarta. Indiya ce ke dakashi 40% na cinikin shinkafa a duniya kuma tana sayar da busasshiyar shinkafa ga kasashen Afirka,musamman Senegal, da Najeriya, da Cote dIvoire  da Benin, da  kasashen Yankin Asiya Pakistan,da Philippines da kuma  Yankin Gabas ta Tsakiya Turkiyya, da Siriya.