Jam'iyyun Najeriya sun fara yakin neman zabe
September 28, 2022A Najeriya ba da izinin fara yakin neman zaben da za'a yi a 2023 da hukumar zaben kasar ta yi ya sanya kara kankaman harkokin siyasa a kasar da alummarta suka dade da jiran wannan lokaci. Ko wadanne batutuwa ne ake sa ran za su mamaye yakin neman zaben a dai dai lokacin da alummar kasar ke matukar samun sauyi na tafiyara da kasar daga ‘yan siyasa?
Fagen siyasar dai tuni yake amo na yakin neman zaben da ‘yan siyasa suka fara daga ranar Larabara nan inda suke alkawura na aiyyukan da za su yi wa jama'a don fitar masu da kitse a wuta daga hali na rayuwa da suke ciki. A tsari na yakin neman zabe dai kamata ya yi a mayar da hankali a kan batutuwa, amma aksin haka akan gani a Najeriya.
Karin Bayani:Tasirin addini a siyasar Najeriya
Kokari ne dai na kaiwa ga madafan iko ta hanyar neman kuri'ar jama'a da tsarin dimukurdiya ya bayar bayan kowane shekaru hudu a Najeriya da dole sai an yi sauyin hannun mulki don a baje a faifai. Injiniya Buba Galadima sakataren kwamitin amintattu na jam'iyyar adawa ta NNPP ya bayyana cewa suna fata kan samun nuna manufofi a yakin neman zaben da za a yi a shekara mai zuwa.
Jam'iyyu 18 ne dai ke neman takara a zaben da za'a yi a shekara mai zuwa, kuma duk na kokuwar kai wa ga mukamin da yafi tsolewa kowa ido na neman zama shugaban kasa a Najeriya. Jamiyyar PDP ita ce jagaba a jerin wadanda ke adawa tare da kokarin karbe mulki daga hannun jam'iyyar APC da ke kan madafun iko.
A bisa dokar zabe dai akwai tsari da ka'ida da doka ta amince da ita domin yakin neman zabe kamar yadda Barrsiter Mainasara Umar masani a fanin shari'a ya bayyana. Manyan jam'iyyun Najeriya dai bas u kaiga kadammara da fara yakin neman zaben ba, domin daga APC zuwa PDP duk haka bagatatan suka dage kadammar da yakin neman zaben bisa dalilai mabambanta.