Janye dakarun Faransa daga Jamhuriyar Nijar
October 10, 2023Wannan na zuwa ne bayan takun saka na sama da watanni biyu da aka share ana yi tsakanin hukumomin mulkin sojan kasar Jamhuriyar Nijar da gwamnatin Faransa. Tuni koma kungiyoyin fafutika da sauran 'yan kasar suka soma bayyana matsayinsu a kai.
Karin Bayani: Nijar: Dakarun Faransa za su fice bisa rakkiyar sojoji
A yammacin wannan Litinin ayarin farko na sojojin Faransa guda daga cikin dubu da 500 ya tashi daga filinin jirgin sama na birnin Yamai zuwa birnin Ndjamena na kasar Chadi. Wannan na zuwa ne bayan kungiyoyin matasa ‚yan fafutika suka kwashe sama da watanni biyu suna zanga-zanga da kuma zaman dirshen a gaban cibiyar sojojin Faransa da ke a birnin Yamai. Malam Falmata Taya ta kungiyar M62 wacce ke a sahun gaban wannan kokowa ta bayyana farin ciki.
A ranar Alhamis da ta gabata dai rundunonin sojin Faransa a nijar da takwarorinsu na Nijar suka cimma matsaya kann jadawali aikin ficewar sojojin na Faransa daga Nijar. A karkashin jadawalin wasu sojojin Faransar za a yi jigilarsu ne da jiragen sama da wasu kayansu. Amma akasarin sojojin za su fice ne daga kasar tare da kayansu ta kasa ne inda za su ratsa yankunan kasar ta Nijar da dama a tsawon kilomita kusan dubu da 800 da suka raba biranen Yamai da na Njanmena a bisa rakkiyar sojojin Jamhuriyar Nijar har kan iyaka.
To sai dai Malam Mohamed Abdoulkader wani mai kusanci da hambararren shugaban kasa na ganin ficewar sojojin Faransar babbar matsala ce musamman ga sojojin 'yan juyin mulki a Jamhuriyar Nijar: