Nijar: Fara bayyana sakamakon zabe
December 29, 2020Ya zuwa karfe 12 na ranar Talata dai, alkaluman sakamakon zaben shugaban kasa wanda hukumar zaben ta wallafa a shafinta na Internet, sun nunar da cewa sakamakon kananan hukumomi 23 ne cikin 266 da ake da su a fadin kasar ne suka shigo hannun hukumar. Ya zuwa yanzu dai, dan takarar shugaban kasa a jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya Bazoum Mohamed ne ke kan gaba da kuri'u dubu 96 da 329, Mahaman Ousmane na jam'iyyar RDR CANJI na bi masa da kuri'u dubu 39 da 261, Seini Omar na jam'iyyar MNSD NASSARA na matsayin na uku da kuri'u dubu 15 da 11, Alma Oumarou na RPP FARILLA na matsayin na hudu da kuri'u dubu 13 da 989.
Karin Bayani: Al'umma na dakon sakamakon zabe a Nijar
A bangaren zaben 'yan majalisun dokoki kuwa, sakamakon farko da hukumar ta bayyana na nuni da cewa jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki na kan gaba a gundumomi da dama amma tana fuskantar kalubale daga jam'iyyun Lumana Afrika da RDR Canji, baya ga yadda wasu kanana da matsakaitan jam'iyyu suka ja zarensu a wasu yankunan. Misali a jihar Dosso, jam'iyyar ANDP ZAMAN LAHIYA na jan zarenta, haka ma abin yake a Jihar Maradi ga jam'iyyar CPR Inganci wacce ta tsaya zaben 'yan majalisa, inda a wasu gundumomi ko jam'iyya mai mulkin ba ta shiga gabanta ba. A cewar shugaban jam'iyyar Malam Kassoum Moctar ya gamsu matuka da yadda sakamakon ke zo musu.
Ya zuwa yanzu dai hukumar zaben ba ta bayyana adadin kujerun da kowacce ja'iyya ta samu a zaben kasar 'yan majalisar ba, tana mai cewa kowace jam'iyya ta san kujerun da ta samu a kowace gunduma, ta la'akari da yawan mutanen da suka kada kuri'a. A wasu yankunan alal misali dan kujerar majalisa ke kai kuri'u dubu 30 zuwa sama a yayin da a wasu yankunan da kuri'un da ba su kai haka ba ma, mutun ka iya samun kujerar majalisa.
Karin Bayani:Ana ci gaba da zabe a Jamhuriyar Nijar
Daga cikin kujeru 171 da majalisar ta kunsa, birnin Yamai na da kujeru 10 Jihar Tillabery na da 23, Dosso na da 19, Tahoua na da 'yan majalisa 30, Maradi 31, Damagaram 32, Diffa bakwai yayin da Agadez ke da guda shida. Al'ummar Nijar mazauna kasashen waje ma ba a bar su a baya ba, domin suna da kujeru biyar, sai kuma kujeru dai-dai a mazabun musamman guda takwas na Banibangou da Bankilare da Bilma da Tesker da Tassara da Ngourti da Bermo da kuma Makalondi. Hukumar ta CENI dai na ci gaba da tattara sakamakonzaben na shugaban kasa da na 'yan majalisu, tare da wallafa su lokaci zuwa lokaci, inda ta ce ta sa ran cin karfin sakamakon a tsawon yinin wannan Talata zuwa safiyar Laraba mai zuwa.