1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jakadan Faransa a Nijar na cikin koshin lafiya

Abdoulaye Mamane Amadou ARH
September 3, 2023

Gwamnatin Faransa ta ce jakadanta a Nijar yana cikin kofin lafiya tare da samun tabbataccen tsaro a fadar gwamnatin kasar Niamey, duk da matsin lambar da sojojin Nijar ke yi masa na ficewa daga kasar.

https://p.dw.com/p/4Vu2S
Niger I Zanga-zanga I Adawa da sojojin Faransa
Niger I Zanga-zanga I Adawa da sojojin FaransaHoto: AFP

A wata hira da jarda a kasar Faransa "Le monde" a ranar Lahadi, ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna, ta ce "Ba za mu laminta da wata bukatar wani ministan da bai da wani hurumi a garemu ba." 

Mrs. Colonna ta kara da cewa "Jakadan ne wakilinmu a wajen gwamnatin da ke da cikakken 'yanci jagoranci Nijar, ba wai sojojin da suka murde mulki da tsinin bundiga ba."

Karin Bayani:Boren kin jinin sojan Faransa

Kalaman ministar na zuwa ne a daidai lokacin da aka shiga rana ta uku ta zanga-zangar kin jinin sojin Faransa a Nijar da wasu kungiyoyin fararen hula masu da'awar goyon bayan sojin da suka karbe mulki suka shirya a gaban sansanin sojojin Faransa da ke birnin Niamey.

Zanga-zangar na zuwa ne bayan gwamnatin Paris da Niamey na yi wa juna kallon hadirin kaji, tun bayan korar jakadan Faransa a Nijar da gwamnatin Abdourahmane Tchiani ta yi jim kadan bayan karbe iko, matakin da fadar mulki ta Elysee ta yi fatali da shi.

Akalla soji 1,500 ne Faransar ta jibge a Jamhuriyar Nijar domin yaki da 'yan ta'adda a yankin Sahel, yakin da masu tsananin adawa da sojan ke cewar ba su tsinana wa Nijar komai ba ta fannin tsaro.