1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Zanga-zangar adawa da gallazawar 'yan sandan a Faransa

Binta Aliyu Zurmi
September 24, 2023

Dubban mutane a Faransa sun gudanar da zanga-zanga bijirewa gallazawar 'yan sanda ga al'umma, Watanni uku bayan wacce ta gudana biyo bayan kisan wani matashi da jami'in tsaro ya yi.

https://p.dw.com/p/4Wk8E
Frankreich | Proteste gegen Polizeigewalt in Paris | Ausschreitungen
Hoto: Olivier Arandel/MAXPPP/dpa/picture alliance

Boren da masu sasaucin ra'ayi suka shirya, ya sami halarta sama da mutum dubu 80,000 a daukacin kasar yayin da a birnin Paris jami'an tsaro suka ce wasu mutum dubu 15 ne suka fita tituna, sai dai anyi taho mu gama tsakanin jami'an da masu boren.

Zanga-zangar na zuwa ne wata uku bayan wacce aka yi sakamakon kisan da dan sanda suka yi wa wani matashi da ya ki tsayawa a lokacin bincike ababen hawa a Paris.

Masu boren sun nuna adawa da dokar tsaro mai lamba 435-1 wacce aka samar a shekarar 2017, da ta bai wa jami'an tsaro damar harbe duk mutumin da bai bi umarninsu ba.


Dauke da allunan rubutu, mutane manya da kanana na masu cewar ba za su manta da abin da ya faru ba kuma ba zasu yafe ba, dokokin kasar nan na kashe mutane.

Faransa dai ta jima tana fuskantar bore inda a lokuuta da dama kan janyo arangama tsakanin al'umma da jami'an tsaro.