1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Farfado da tattalin arziki

May 21, 2020

Hukumomi a tarayyar Najeriya sun kama hanyar sake farfado da tattalin arzikin kasar da ke cikin wani mawuyacin hali sakamakon bullar annobnar Covid-19.

https://p.dw.com/p/3cah1
Nigeria Abuja | Prsident Muhammadu Buhari ernennt Ibrahim Gambari zum Stabschef
Hoto: Reuters/Nigeria Presidency

Yawan kudin da tarrayar Najeriyar ta gani a cikin watannin farko na wannan shekarar ciki har da na man fetur ba su wuce Billion 940.91 ba, adadin da ke zama kasa ga kaso 31% na kudaden shiga da kasar ta yi fatan samu a baya.

Ko da yake a kashi na biyu na wannan shekarar ana sa ran adadin kudin shigar zai kasance mafi tasiri ga tattalin arzikin kasar, inda ake hasashen zai kasi tsakanin kaso 4.4% zuwa kaso 8.9% biyo bayan bulluwar annobar coronavirus ta shafi fannonin kiwon lafiyar kasar da ma wasu fannoni dabam-dabam. Tuni majalisar tattalin arzikin Najeriya ta amince da a sake bude harkoki na tattalin arzikin kasar da zummar daukar matakan kaucewa bala'in dake tunkarar kasar sakamakon tasirin annobar coronavirus.

An gudanar da taron farko ta kafar sada zumunta kan wannan batun, wanda ya hada gwamnonin kasar da gwamnatin tarrayar Najeriya, taron ya kuma tabbatar da cewa sun amince da a fara aikin sake bude tattalin arzikin kasar baki daya duk da karuwar annobar da ke iya kaiwa dubu 300 kafin karshen watan Augusta.

Duk da yake cewa sai a cikin watan Yuni´aka yi hasashen za a fara jin radadin kaifin annobar a tsakanin gwamnatocin jihohin kasar, tuni wasu jihohin suka fara rage albashin ma'aikata dama rage adadin kudaden da suke kashewa da nufin tsira daga dan abinda ya rage a aljihunansu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu kan wata doka da za ta bai wa gwamnatin kasar damar kwace kudade da kaddarorin 'yan kasar dake waje, wadanda Najeriyar ke zargin wasu 'yan kasar sun sace kuma sun boye a bankunan kasashen duniya.