Farfesa Jega na son a yi watsi da jam'iyyun Najeriya
August 3, 2021Daya dai ta share shekaru 16 a cikin 60 da ta ce z ata kwashe tana mulki kafin ya kubuce mata, daya kuma na shirin ta kai takwas a gadon mulkin Najeriyar. Sai dai kuma daga dukkan alamu daukacin manyan jam'iyyun kasar guda biyu sun bata rai cikin kasar da ke fadin ana bukatar sauyi.
Kuma na baya baya cikin masu karatun da ta sauyar na zaman tsohon shugaban hukumar zaben Tarrayar Najeriyar farfesa Attahiru Jega. Farfesan da ya jagoranci nasarar karshen ‘yan lemar sannan kuma ya kai ga haihuwar mulkin na masu tsintsiya dai, ya ce daukacin jam'iyyun kasar guda biyu sun kasa.
Jam'iyyun guda biyu dai a tunanin farfesa Jega na zaman ‘yan biyu ga batun cin hanci da gazawa, a saboda haka akwai bukatar ‘yan kasar su kaurace musu yayin babban zabe na shekarar 2023. Kalamansa dai na kara fitowa fili da irin fasalin da siyasar kasar take shiri da ta dauka tun kafin babban zaben da ke da muhimmanci ga makomar kasar.
Buba Galadima dai ya share shekaru 20 da doriya yana ta adawa kuma a fadarsa jam'iyyun guda biyu na kama da kungiyoyi na asiri maimakon jam'iyyu na siyasa. Wandaka a ganimar yaki ko kuma kunne na uwar shegu da bukata ta ‘yan kasa dai, daukacin jam'iyyun guda biyu dai sun hau mulki a bisa ga kokari na tunkarar muhimman matsalolin cin hanci da batu na tattalin arziki da ma zamantakewa a kasar.
To sai dai kuma an share shekarun jam'iyyun guda biyu tare da nuna alamun lalacewar lamura na kasar maimakon sauyin da ke zaman alkawari a tsakanin talakawa da masu mulkin Najeriyar.
Kuma a fadar Tanko Yakasai da ya faro tun daga dauri, Najeriyar tana bukatar sabuwar jam'iyya ta gaskiya cikin ta.
A shekara ta 2014 ne dai masu adawar Najeriya suka kai ga kau da bambancinsu, suka kuma kafa jam'iyyar APC da ta yi nasarar karbe goruba a hannun kuturu.
To sai dai kuma a fadar Saidu Bello, jigon jam'iyyar PDP, da kamar wuya ai nasarar iya samar da sabuwar jam'iyya ga kasar a cikin tsarin da siyasar ke neman komawa ta kabila maimakon tsarin shan koko mai kama da kokarin daukar rai.