1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargaba dangane da lafiyar Shugaba Buhari

April 28, 2017

A wani abin da ke iya kaiwa ga kara jefa damuwa a zukatan al'umar tarrayar Najeriya, an kai tsawon mako guda ba tare da ganin shugaban kasar Muhammad Buhari a bainar jama'a ba.

https://p.dw.com/p/2c6Ib
Äthiopien Gipfel Afrikanische Union - Muhammadu Buhari
Hoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

An dai dauki lokaci ana kace-nace game da batun lafiyar shugaban tarrayar Najeriya da ke kara nuna alamu na kauracewa bainar jama'a. Daga dukkan alamu rudanin yana shirin kara karuwa bayan share tsawon wannan mako ba tare da ganin shugaban a cikin jama'a ba.

Bayan kauracewa halartar taron majalisar kasar na mako-mako cikin tsakiyar wannan mako dai, bangaren gwamnatin na kafa hujja ne da zabi na shugaban na yin aiki ko dai daga kuryar daki ko kuma a cikin ofishin da gwamnatin kasar ta gina domin aikin nasa.

To sai dai kuma gaza baiyyanarsa a sallar wannan Juma'a  dai na neman kara girman damuwar tsakanin ‘yan kasar da a baya ke iya tozali da shi koda kuwa sau guda ne a cikin mako.

Shugaba Buhari dai ya yi bayyanarsa ta karshe a bainar jama'a ne a ranar Juma'ar makon jiya a massalacin fadar gwamnatin kasar ta Aso Rock. To sai dai kuma a fadar kakakin gwamnatin Malam Garba Shehu ba a nan gizo ke sakar ba game da lafiya ko akasin haka ta shugaban.

 

Dawowarsa daga Jinya

Afrika Nigeria - Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: Reuters/Stringer

A ranar 10 ga watan jiya na Maris ne shugaban kasar ya dawo daga wani hutu na magani na wattani kusan Biyu. Duk da cewar ya nuna alama ta kuzari daga farkon fari, karin janyewar na kara sanya damuwa ga ‘yan kasar da ke da tunanin zahiri na halin lafiyar jagoran sauyin nasu.

Tarrayar Najeriya dai ta shiga rudani sakamakon rashin lafiya ta tsohon shugaban kasar Umar Musa Yar'adu'a , da ya rasu a gadon mulki shekaru bakwai can baya.

Tuni dai wasu a cikin ‘yan kasar da suka hada da shahararren marubucin nan Wole Soyinka suka nemi shugaban kasar daya bayyana halin lafiyar tasa.

Bai dai kamata shugaban kasar ya rika boye hali na lafiyarsa kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ke boye batu na harajinsa ba, a cewar Soyinka.

To sai dai kuma a fadar malam Garba Shehu babu abin boyo ga lafiyar ta shugaban kasa da ke zaman harka ta kashin kai da kuma zabin da ke a hannu na shugaban kasar ba wani ba.

Abin jira a gani dai na zaman tasiri na sabuwar takaddamar ga batun mulki da siyasar Najeriyar da ke kara fuskantar yanayi na siyasa a cikin hali na ta ci bata ci ba ga lafiyar ta shugaban kasa.