Haiti: Fargabar dagulewar al'amura
March 5, 2024Sojoji da 'yan sandan Haiti sun yi bata-kashi da gungun 'yan daba masu tayar da tarzoma da yunkurin hargitsa kasa, jim kadan bayan da hukumomin kasar suka sanar da dokar hana fitar dare. Babu cikakkun bayanai, dangane da wadanda suka rasa rayukansu ko kuma jikkata. Matakin sanya dokar hana fitar ya biyo bayan yadda maharan dauke da makamai suka fasa manyan gidajen yarin kasar guda biyu a karshen makon jiya, inda suka saki dubban fursunonin da ke daure a ciki da suka kunshi wadanda suka aikata miyagun laifuka dabam-dabam da suka hadar da kisan kai da garkuwa da mutane. Haka zalika a makon jiyan sun durfafi filin jirgin saman Port-Au-Prince da harbe-harbe, amma ba su samu damar kutsawa ciki ba inda tuni aka sanar da rufe shi. Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guturres ta bakin mai magana da yawunsa Stephane Dujarric ya bukaci kasashen duniya su hanzarta bayar da kudin agaji, domin kubutar da kasar daga hannun mahara masu dauke da makamai da ke yunkurin daidaita kasar.
A yanzu suke da ikon kaso 80 cikin 100 na Port-Au-Prince, babban birnin kasar kuma suke kokarin tunkarar babban bankin kasar. Tuni dai ministan kudin kasar Patrick Boivert da kuma ke rike da mukamin firaministan kasar, ya umarci 'yan sanda da sojoji da ma sauran jami'an tsaro da su yi amfani da duk wata dama da suke da ita wajen tabbatar da wanzuwar tsaro da zaman lafiya ta hanyar dakile ayyukan maharan. Shi dai firaministan kasar ta Haiti Ariel Henry a yanzu haka yana bulaguro a Kenya da nufin neman agaji a fannin tsaro, domin murkushe masu boren. Kenyan dai ta amince da bayar da tallafin 'yan sanda 100 kana Jamhuriyar Benin za ta ba da dubu 1,500, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar. Yayin da ake dakon kasashen Bahamas da Bangladesh da Barbados da kuma Chadi, domin jin irin nasu taimakon.