1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haiti: An samu tsohon sanata da laifin halaka tsohon shugaba

October 11, 2023

Tsohon sanatan na kasar Haiti ya fallasa yadda ya tallafa wa mhara kashe tsohon shugaban kasar.

https://p.dw.com/p/4XNrO
Hoto: Matias Delacroix/AP/picture alliance

Tsohon sanata a kasar Haiti Joseph Joel John ya amsa laifin sanya hannu wajen yi wa tsohon shugaban kasar Jovenel Moise. Joel John shi ne babban mutum na uku da ya amsa laifin taimakawa wajen hallaka tsohon shugaban a shekara ta 2021.

Bayanan da tsohon sanatan na Haiti ya mika wa wata kotu da ke zaune a birnin Florida na Amirka, inda a nan ne aka kisa yi wa tsohon shugaban kisan gilla, Joel John ya ce laifukansa sun hada da bai wa makasan shugaban hayar motoci tare da tsara yadda za a yi kisan.

Alkalin kotun ya bayyana ranar 19 ga watan Disamba a matsayin ranar da zai ayyana hukunci ga tsohon sanatan da ke cikin mutum 11 da ake zargi da kashe tsohon shugaban kasar Haitin da ke yankin Caribbean.