Jamusawa ka iya daskarewa yayin hunturu
July 11, 2022Akwai dai fargaba da ma rashin tabbas kan sake bude bututun, inda ake ganin mahukuntan Moscow sun dauki matakin gyaran ne domin cimma wata manufa ta siyasa. Ita dai Rasha ta rufe bututun gas da ke kai wa kasar Jamus iskar gas din ne saboda abin da ta kira gyare-gyare da aka saba lokaci zuwa lokaci.
Karin Bayani: Kammala taron koli na kasashen G7
Saidai a wannan karon Jamus tana zargin Rasha da amfani da damar domin cimma manufar siyasa sakamakon yakin da ta kaddamar a kan Ukraine, inda sauran kasashen yammacin duniya ke taimakon Kyiv. Claudia Kenfert ita ce shugabar bangaren makamashi da sufuri gami da muhalli a cibiyar nazarin tattalin arziki ta Jamus, kumna acewarta tuni aka rage yawan gas din da ake amfani da shi a kasar.
#b#Masu haya da dama a Jamus sun samu takardun karin kudin makamashi, abin da ke kara irin kudin da mutane ke kashewa. Misali a birnin Berlin fadar gwamnati, akwai inda aka samu tashin farashi na kashi 100 bisa 100 a wasu gidaje. Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce babu wata kasa a duniya da za ta iya dakile tashin farashin da ke faruwa ita kadai ko ba da tallafi, sai dai gwamnati tana karfafa gwiwar rage amfani da makamashi.
Karin Bayani: Sharhi kan kwanaki 100 da mamaye Ukraine
Shi kansa Robert Habeck mataimakin shugaban gwamnati kana ministan kula da tattalin arziki, ya ce abin da Rasha ke neman yi ya saba da doka. Muddun Rasha ta kaste gas ga Jamus baki daya haka zai shafi daukacin tattalin arzikin kasar, akwai fargabar tattalin arzikin Jamus zai iya smun koma-baya da kimanin sama da kaso 12 cikin 100 zuwa karshe shekara. Dama dai tuni annobar cutar corionavirus, ke janyo raguwar tattalin arzikin Jamus din da sama da kaso tara cikin 100 a duk shekara bayan samun bullar cutar.