Olaf Scholz zai kai ziyara birnin Kyiv
June 15, 2022An dai yi ta samun sabani kafin shugabannin uku su yanke shawarar kai ziyarar. Jakadan Ukraine a Jamus Andriy Melnyk yana sa ran cewa shugaban gwamnati Olaf Scholz zai sanar da wani sabon kunshin taimakon kayan yaki a ziyarar da zai kai birnin Kyiv, wanda zai iya hadawa da manyan tankunan yaki da motocin sulke. Wasu majiyoyi a Kyiv sun ce Ukraine na bukatar manyan bindigogi guda 1,000 da rokoki 300 da tankunan yaki 500 da motocin sulke 2,000 da jirage marasa matuka 1,000, domin tinkarar dakarun Rasha a yankin Donbas. Da ma a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta ZDF a Jamus, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya bukaci goyon bayan Scholz da gwamnatinsa domin samun makaman da dakarunsa ke bukata cikin gaggawa.
KarinBayani: Kasafin kudin Jamus ya karu
Sojojin Rasha sun harba makamai masu linzami fiye da 2,600 a biranen Ukraine, tun bayan mamayar da suka fara a watan Fabrairun wannan shekara. Ko da jakadan Ukraine a Jamus, Andriy Melnyk sai da ya ce kasarsa ta yi asarar sojoji a wannan yakin. Olaf Scholz na Jamus ya samu goron gayyatar zuwa Kyiv da jimawa, amma wasu dalilai suka hana shi zuwa. Da farko dai a watan Afrilun wannan shekara, gwamnatin Ukraine ta ki bai wa shugaban Tarayyar Jamus Frank-Walter Steinmeier damar ziyartar Kyiv, saboda zarginsa da kusanci da fadar mulki ta Kremlin. Saboda hake ne Scholz da aka bai wa izini ya yi dari-dari, sakamakon cin mutumci kasarsa da Ukraine ta yi. Hasali ma jakadan Ukraine a Jamus Andriy Melnyk ya ci gaba da ta'azzara rikici, inda ya furta kalaman da suka saba da diflomasiyya a game da Scholz.
Sai dai a karshe, Shugaba Steinmeier na Jamus da Zelensky na Ukraine sun fahimci juna bayan da suka tattauna tsakaninsu, sai dai hakan bai hana shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz din ci gaba da nuna shakku ba. Shugaban jam'iyyar adawa ta CDU Friedrich Merz ya kasance na farko daga Jamus ta ya ziyarci Kyiv. Ita kuwa Annalena Baerbock ministar harkokin waje, ta zama babbar jami'ar gwamnatin farko da ta yi tattaki zuwa Ukraine a watan Mayu. A lokacin dai, firaministan Biritaniya Boris Johnson ya riga ya kai ziyarar ba-zata, tare da yi wa hukumomin Ukraine jerin alkawura na kara yawan tallafin soja da na tattalin arziki da kuma hada kan kasashen duniya domin kawo karshen yakin.
KarinBayani: Tasirin rikicin Rasha da Ukraine a Afirka
Akwai Bambanci kamun ludayi tsakanin Olaf Scholz da sauran shugabannin kasashen yammacin duniya. Gwamnatocin Birtaniya da Amirka da kasashen gabashin Turai sun bai wa Ukraine gudunmawar kayan aikin soji da yawa kuma da wuri, a daidai lokacin da Scholz ke gargadi game da barazanar fara yakin duniya na uku. Hasali ma ya fara aika wa Ukraine da manyan makamai ne, lokacin da matsin lamba musamman daga Washington ya yi yawa. Amma baya ga tankokin yaki da ya mika, sai a kwanan baya ne shugaban gwamnatin na Jamus ya yi alkawarin bayar da na'urorin harba makaman roka guda hudu. Ya zuwa yanzu dai, kanana makamai da harsasai ne kawai suka isa Ukraine. A wani taro a Vilnius a makon da ya gabata tare da shugabannin kasashe da gwamnatocin Lithuania da Latvia da Estoniya, Olaf Scholz ya sha suka a gabashin Turai. Su dai kasashen da ke cikin tsohuwar Tarayyar Soviet, na fargabar zaluncin Rasha idan Putin ya yi nasara a Ukraine.