Fargabar rikicin bayan zabe a Najeriya
December 29, 2014Masu ruwa da tsaki a harkokin zaben da aka tsara farawa a tsakiyar watan Fabarairun shekara mai zuwa, na fargabar sake barkewar rikici bayan zabukan na 2015. Daruruwa na rayuka ne dai suka salwanta cikin kasar da ta kalli tashi na hankali jim kadan da kamalla zabuka a shekaru kusan hudun da suka gabata. A wani abun da ya bude sabon babi kuma ya dora kasar bisa taswirar zub da jini a cikin harkoki na siyasa, abun kuma da har ila yau ya kalli kokari daga sassa daban-daban na masu ruwa da tsaki da batun zaben, wanda kasa da watanni biyu da shirin sake fafatawa ke neman mafitar kaucewar rikicin da tuni ya fara nuna alamar sake kunno kai.
Tun ba'a kai ga ko'ina ba dai aka fara samun rahotanni na zubar da jini da kalamai na rashin hakuri a tsakanin magoya baya dama shugabanni na siyasar a matakai daban-daban cikin kasar. Kama daga Asari Dokubo da ke fadin sai Jonathan ko kafar katako, ya zuwa ragowar magoya baya na arewa da suka dauki sana'ar jifa da nufin tsoratar da masu adawa da tunanin ko Buhari ko akai ga rijiya dai, tuni hadarin rikicin ya kai ga haifar da damuwa a zuciya irin ta su mataimakin shugaban kasar Namadi Sambo wanda ya ce wasu tun yanzu suna maganganu na jawo tashin hankali wadanda suka janyo aka samu tashin hankali a baya hakan kuma bai kamata ba, yana mai cewa Najeriya ta Musulmi da Kirista ce baki daya.
Siyasar Addini da Bangaranci
Batun Kirista da Musulmin dama arewa ko kudu ne dai ke tsakiyar yakin neman zaben a cikin fagen siyasar da ya sake dora Kiristan karawa da Musulmin da nufin samar da sabon shugaban da zai jagoranci harkokin kasar na shekaru hudun da ke tafe. Da dama a sassa na arewacin Najeriyar dai na kallon gazawar shugaban kasar na tunkarar matsalar rashin tsaro da baki na wuta, wanda hakan ya sanya zaben kasar da ke tafe a matsayin magana ta tabbatar da makoma maimakon zabe na shugaba, a yayin kuma da kananan kabilun da ke kudu ke yiwa shugaban kallo irin na jagoran da ya kama hanyar ceto su a hannun manyan kabilun kasar da ke musu danniya na lokaci mai nisa. To sai dai kuma a fadar Sambo batun Musulmi da Kirista a siyasa ta kasar dai na da tsohon tarihin da ya kai tun daga 'yancinta.
Siyasar Addini ta samo asali a Najeriya
"Tun da aka fara siyasar Najeriya ake samun in shugaban kasa Musulmi ne Kirista ne zai taimaka masa, Tafawa Balewa shine shugaban kasa Zik ne mataimakinsa, Shagari Ekweme ne ke taimaka masa. Yau kuma ni Namadina, Na Madinan Madina nine mataimaki. To ya mutane zasu rika raba kan mutane da siyasar addini da sauransu."
Namadinan Musulunci ko kuma Namadinan PDP dai, ruwan da yai maka sharkaf a tunani na masu siyasa a kasar ne ya kamaci jan gaba ga kokari na ci gaba, abun kuma da a cewar Sambon na nan ta ko'ina cikin kasar ga kowa ya gani. Abun jira a gani dai na zaman mafita ga masu siyasar da ke fitar da dabaru iri-iri da nufin neman goyon baya da hadin kan neman damar mulkin kasar na shekarun da ke tafe.