Najeriya: Barazanar karancin abinci
January 8, 2025To sai dai kuma tun ba a kai ko'ina ba dai kasar na fuskantar barazanar komawa cikin gidan jiya, sakamakon kwashe abinci da kai shi kasashe makwabta da ma sassa dabam-dabam na duniyar Allahu. Rushewar darajar Naira da bukata ta kudi dai, ya farfado da kasuwa ta abincin. Buhari Abdullahi dai na sana'ar kai abincin zuwa Nijar, kuma ya ce da fa'ida cikin sana'ar tasu.
Kokari na neman riba ko kuma rikici cikin batu na abinci dai, an dai kai kakar daddafe sakamakon hauhawar farashin abinci da ta tayar da hankalin miliyoyin al'ummar kasar. Hauhawar kuma da ke shirin dorawa, sakamakon kwashe abincin zuwa kasashen waje.
Mohammed Magaji dai na zaman kakakin kungiyar Manoman Tarayyar Najeriyar, wanda kuma ya ce dole kanwar naki ce ke sanya masu noman sai da hajjar tasu. In har manoman Najeriyar suna murnar karba a cikin kaka, daga dukkan alamu suna shirin ji a jiki a nan gaba kan hanyar ta ci-da-kai da ke zaman babban kwazo. Najeriyar ta kashe Naira tiriliyan daya da miliyan dubu 700, a watanni shida na farko na shekarar da ta shude wajen shigo da abinci.
Dakta Hamisu Yau dai na zaman kwararre ga tattalin arziki da kuma ya ce kasar tana shirin dorawa a tsada ta abinci duk da karuwar ta abincin da ta samu a kaka ta bana. Har ya zuwa yanzun dai baabu alamun sauka ta hauhawar ta abinci da ta kusan kaso 40 cikin 100, kuma ke tayar da hankalin yan mulki na kasar.