Fargabar ta'azzarar rikici bayan kisan Nasrallah
September 28, 2024Iran na cikin kasashen farko da suka yi gargadi da babbar murya ga Isra'ila a ta bakin mataimakin shugaban kasar na farko Muhammad Reza Aref na cewar kisan da aka yi wa shugaban kungiyar Hizbollah Hassan Nasrallah a wani hari ta sama da aka kai a kudancin babban birnin kasar Lebanon zai kawo rugujewar Isra'ilar.
Tehran din dai ta sanar da cewar wani fitaccen janar a rundunar juyin juya halin kasar ya mutu tare da jagoran Hezbollah a Beirut. Kamfanin dillancin labaran Iran ya ce an kashe Abbas Nilforushan mai shekaru 58, mutumin da ke cikin jerin wadanda Amurka ta kakaba wa takunkumi a shekarar 2022, wanda kuma ya goyi bayan yakin basasar Siriya da aka fara tun 2011:
Ga dai abun da Marigayi Janar Abbas ya fada a baya " Mun kulla damarar yaki da makiya. Ba ma jiran sai an kawo mana hari, daga wadanda ke kashe har jarirai balle mukai harin ramuwar gayya, watakila za ku shaida haka da martanin da muka yi bayan mugun abu da suka aikata a bara, kuma muka ci gaba da martani".
Tsohon fraministan Lebanon Saad al-Hariri, ya ce kisan Sayyed Hassan Nasrallah ya jefa kasar Labanon da ma yankin gaba dayansa cikin wani sabon yanayi na tashin hankali, wanda suka yi tir da kashe-kashen rayukan fararen hula a lokacin da ake amfani da kisa a matsayin makami na siyasa. Kungiyar Houthi ta kasar Yemen ta yi jimamin kisan Nasrallah, inda ta kara da cewa shahada da yayi za ta karfafa sadaukarwa da ci gaban gwagwarmaya.
Sai dai Isra'ilar a nata bangaren ta cehare haren da ta kaddamar a Lebanon somin tabi ne cikin jerin manufofin da ta sanya a gaba, a ta bakin hafsanta na soji Herzi Halevi:
"Mun kuduri aniyar ci gaba da ruguza kungiyar ta'addanci ta Hizbollah da kuma ci gaba da yaki. Muna da karin ayyuka a gaba a fannoni masu yawa, ruguza kungiyoyin ta'addanci da karya lagonsu, da kuma mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su. Wannan ita ce manufar. Kazalika da mayar da mazauna yankuna arewaci da kududanci gidajensu lafiya."
Amurka dai ta ce ta kuduri aniyar hana Iran da kungiyoyin da ke samun goyon bayanta yin amfani da halin da ake ciki a Lebanon wajen fadada rikici, kamar yadda sakataren tsaron kasar Lloyd Austin ya shaida wa takwaransa na Isra'ila Yoav Gallant a wata waya a jiya Juma'a.
A yayin da take sukaraika aikan Isra'ila, ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta bayyana halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya bayan mutuwar Nasrallah da cewa yana da matukar hadari ga makomar yankin baki dayansa.
Ministan lafiya a Lebanon Dr Firas Abiad ya ce asibitoci na neman kasawa a Beirut a wannan rikici da tuni ya kashe mutane dubu 1,640 ciki har da yara 104 da mata 194, sannan wasu 8,408 suka jikkata.
Da ranar yau ne dai Kungiyar Hizbollah mai samun tallafi da goyon baya daga Iran, ta tabbatar da kashe Hassan Nasrallah, bayan da Isra'ila ta ce ta kawar da shi a wani harin da ta kai ta sama a sansanin kungiyar da ke yankin kudancin birnin Beirut.