1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

'Isra'ila za ta ci gaba da yakar Hezbollah'

September 26, 2024

A wata sanarwa da Firaminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fitar, ya ce sai kasarsa ta ga bayan Hezbollah.

https://p.dw.com/p/4l78o
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin NetanyahuHoto: Ohad Zwigenberg/AP/picture alliance

Isra'ila ta yi fatali da bukatar wasu kasashen duniya ciki har da babbar mai goya mata baya Amurka ta tsagaita wuta a Lebanon har tsawon kwanaki 21.

Tel Aviv ta lashi takobin ci gaba da barin wuta a kan Hezbollah har sai ta ga bayan kungiyar, musamman ma kwamandojinta da ke yaki.

Karin bayani: Kokarin yayyafa ruwan sanyi ga rikicin Isra'ila da Hesbollah

Luguden wuta da kasar ta kaddamar kan Lebanon da ke zamar tungar Hezbollah ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane a wannan makon, a yayin da ita kuwa kungiyar ta mayar da martani da ruwan rokoki cikin Isra'ila.

Karin bayani: Sabbin hare-haren Isra'ila sun sa 'yan Lebanon tserewa

Tun da farko ma dai ofishin Firaminstan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya fitar da wani sako inda ya ce bai mayar da martani ga sakon bukatar tsagaita wutar ba, kuma ya umarci sojojinsa su ci gaba da bararraka wuta babu kakkautawa.