Najeriya: An samu karin matatar man fetur
December 31, 2024A tsakanin wasu matatu guda biyu na Fatakwal da ta Warri da kamfanin man Tarayyar Najeriya na NNPC ya yi nasarar tayarwa dai ana shirin ta ce karin ganga akalla 117,000 a kusan kullum. Ko bayan matatar Dangote da ke da karfin ta ce ganga dubu 650 dama wasu kanana guda Ukun da ke taka rawa, duka a kokari na wadatar mai a Najeriya da kila ma a makwabta.
A Najeriya da a baya ta ce tana shan lita miliyan 60 na tattacen man domin amfanin al'ummarta, Duk da cewar dai kamfanin Dangoten da kila ma NNPC sun baiyana sai da man zuwa kasashe na waje, akwai dai fatan karuwar ta ce man cikin gida na iya shafar yawa da kila ma farashi a kasuwa. Tun ba'a kai ga k o'ina ba dai ana kallon alamu na takara mai zafi cikin batu na farashi a tsakanin Dagoten da ya karya farashin zuwa 935 a lokutan bukukuwa na kare shekara da kamfanin NNPC da ya rage zuwa 965. Koma wane tasiri 'yan kasar suke shirin gani cikin hajjar man, ita kanta takara tsakanin Dangoten da kamfanin NNPC na da illar gaske ga makomar masana‘antar da ta dauki lokaci tana zaman musababbin kisan dubban miliyoyi na kasar. Har yanzu dai ana takkadama cikin gidan alkali tsakanin bangarorin guda biyu a wani abun da ke zaman kana gani kana dada rudewa.
Dr Garba Malumfashi dai kwarrare ne cikin batun makamashin da kuma ya ce ana da bukatar aiki tare da nufin cika burin sauki cikin farashin mai a kasar. Sauke nauyin man bisa wuya na gwamnatin dai na nufin ceto tattali na arzikin kasar da ya share shekaru yana kisan kudi ba adadi a cikin sunan wadatuwar man fetur. Ya zuwa watan Nuwamban da ya shude dai Tarayyar Najeriya kan kashe abun da ya kai dalar Amurka miliyan dubu 15 ko kuma kaso kusan 20 cikin dari na yawa na kudadenta wajen shigo da hajjar man a shekara.