1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fina-finan da za su yi zarra a 2023

Abdul-raheem Hassan MAB
January 27, 2023

Bayan faduwar kasuwannin CD da DvD, fina-finan Hausa sun koma YouTube da salon dogon zango wato "web series". Sai dai kasuwar ta zama iya ruwa fidda kai, ko kwalliya na biyan kudin sabulu?

https://p.dw.com/p/4MMMZ
Fuskokin wasu taurarin da ke hasakawa a shirin LabarinaHoto: Isa Bawa Doro/Kannywood

Ya yi wuri a iya gane zakaran gwajen dafi na fina-finan Hausa a shekarar 2023, amma masu iya magana suka ce "Jumma'ar da za ta yi kya daga Laraba ake gane ta". Masu sharhi kan fina-finai a arewacin Najeriya sun ce da sauran tafiya a wannan shekarar, amma karbuwar fina-finan da aka fara haskawa a 2022 su ne tabbacin wadanda za su ja akalar masu kallo a Youtube a shekarar bana.

Nigeria Kannywood Film
Darakta Aminu Saira yayin daukar shirin LabarinaHoto: Isa Bawa Doro/Kannywood Multimedia

Labarina: Yadda kamfanin Saira Movies ya ja fim din fiye da yadda ake tsammani, yana cikin abin da ke ci-gaba da jan hankalin masu kallo a shekarar 2023. "Mutane da dama suna tsammanin za a kawo karshen shirin, amma Allah ya sa har yanzu yana jan hankali, kuma yana tasiri tsakanin masu kallo" a cewar Muhsin Ibrahim, mai sharhi kan fina-finan hausa kuma malami a jami'ar birnin Cologne da ke kasar Jamus.

Duk da shirin ya samu sabon marubuci bayan na farko wato Ibrahim Birniwa da kuma sauya babbar jarumar shirin Sumayya, wato Nafisa Abdullahi da Fati Washa, fiye da mutane 500,000 ne ke kallon shirin a YouTube a duk lokacin da aka dora sabon shiri. Wannan na tabbatar da cewa shirin Labarina yana cikin fina-finai masu dogon zango da za su ja akalar masu kallo a 2023, duk da cewa wasu na ganin cewa lokaci ya yi da ya kamata a kawo karshen labarin shirin.

Nigeria Kannywood Film l Izzar So
Wasu jaruman shirin Izzar SoHoto: Isa Bawa Doro/Kannywood Multimedia

Izzar So: Tun bayan mutuwar daraktan fim din Nura Mustapha Waye a shekarar 2022, jama'a suna sa ido su ga ko sabon daraktan shirin zai sauya akala daga yadda marigayi ya bari. Shirin yana samun maso kallo fiye da rabin miliyan a duk lokacin da aka dora shi a tashar BAKORI TV a Youtube. 

Amma da alama karsashin shirin ya fara raguwa a gurin masu kallo saboda fim din ya fara rasa alkibla. Malam Muhsin ya yi shagube kan abin da Lawan Ahmad mashiryin shirin ke cewa: "Ban san ranar gama Izzar So ba" . Malamin ya kara da cewa:  "Duk abin da ka fara, ya kamata ka ce ga ranar da za a gama." . Muhsin ya ce "kwanan nan muka ga Falalu A. Dorayi ya kammala shirin Gidan Badamasi. Haka ya kamata."

Alaqa: Wannan shi ne fim na farko mai dogon zango da kamfanin FKD ya fara shiryawa. Karbuwar fim din a lokaci kadan na da alaka da kayan aiki masu kyau da aka yi amfani da su da kuma tsari, "shirin ya samu labari mai kyau, wanda mutane da dama ke alakanta shi kai tsaye da rayuwarsu ta yau da kullum" inji Muhsin.

Nigeria Kannywood Währung Änderung Film
Ali Nuhu na ba da umarni a shirin AlaqaHoto: Isa Bawa Doro/Kannywood

Salon sarrafa sabbin jaruman fim din yana burge masu kallo, sannan amfani da gidajen alfarma da tufafi da aka yi amfani da su a shirin ya sa zai yi gogayya cikin manyan fina-finanai masu dogon zango da za su kece raini a 2023. Muhsin ya kara da cewa "Girma da tasirin mai shiyra shirin kuma mai ba da umarni kuma jarumi a fim din Ali Nuhu ya kara wa shirin tasiri."

Ɗan Jarida: Labari ne kan aikin jarida da 'yan siyasa da kamfanin Maishadda Global Resources ya shirya a karon farko a fagen fina-finai masu dogon zango. Tun bayan da aka fara sake tallar shirin, masu kallo suka fara marmarinsa. "Shirin ya karbu sosai tun bayan da aka fara nuna shi a karshen shekarar 2022" a cewar Isa Bawa Doro, mai shirya fina-finai na dogon zango. "Tunda nake Hausa fim, ba a taba biyana kudi mai yawa kamar yadda aka biyani a aikin dan jarida ba. Na samu kudi sama da Naira 200,000." a cewar jarumi Shu'aibu Lawan wanda aka fi sani da Kumurci.

Nigeria Kannywood Film l Dan-Jarida-hausa
Wasu jaruman cikin shirin 'Dan JaridaHoto: Isa Bawa Doro/Kannywood Multimedia

Malam Muhsin na jami'ar Cologne da ke Jamus yana cewa "Yawan masu kallon fim din Ɗan Jarida fiye da 200,000, ya tabbatar da matsayinsa na shiga sahun manyan fina-finan da za su yi zarra a 2023."

Nigeria Kannywood Film
Wasu daga cikin shirin "A Duniya"Hoto: Isa Bawa Doro/CEO Kannywood exclusive multimedia

A Duniya: Fim din ya samu karbuwa kwarai da gaske wurin masu kallo, duba da yadda shirin ya zo da salon labarin abin da ke damun mutane na yawan kwacen wayoyi. Bayan samun fahimtar juna tsakanin masu shirya fim din da gwamnatin jihar Kano a 2022, a karshe an karkata labarin zuwa tona asirin masu aikata laifuka. Wani abin da ya sa fim din farin jini sun hada da salon magana ko inkiya da ake amfani da su a fim din kamar "in da Rabbana" inji Muhsin, inda ya ce wadannan kalamai sun yi tasiri sosai tsakanin matasa.

Nigeria Kannywood Film
Adam Abdullahi Adam (Abale)Hoto: Isa Bawa Doro/CEO Kannywood exclusive multimedia

Bawa Doro ya ce akwai fina-finan da za a fara aikinsu a shekarar 2023, kamar irin su "Guguwa da Matar mutum biyu na kamfanin Kannywood Exclusive da fim din Jagora na Lawan Ahmad, sai Abi duniya a Sannu na kamfanin Dorayi films and Distributing Nig. Ltd da kuma fim din Dare Daya na kamfanin Saira Movies".

Yanzu haka dai a kusan kowace rana, akwai fina-finan Hausa masu dogon zango biyu ko uku da ake nunawa a YouTube. Sai dai yawan fina-finan na rage tasiri da ingancin wasu. Saka tallace-talllace a cikin fina-finan, hanya ce ta samar da kudaden shiga don rage asara. Ba don masu shirya fina-finan na son rika katse masu kallo ba ne a cewar Isa Bawa Doro.