1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar PDP ta lashe kujerar gwamnan Adamawa

April 19, 2023

Hukumar zaben Najeriya INEC ta sanar da Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa da aka karasa a karshen makon jiya.

https://p.dw.com/p/4QGN8
Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Bayan rudanin da ya mamaye zaben gwamnan jihar Adamawa da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, Hukumar zabe ta INEC ta ayyana Ahmadu Umaru Fintiri na Jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben, sabanin sanarwar farko da babban jami'in hukumar ta INEC a jihar ya bayar cewa Aishatu Dahiru Binani ta jam'iyyar APC ce ta lashe zaben.

Hukumar zaben Najeriya INEC da ke kokarin wanke sunan ta daga badakalar da Hudu Ari kwamishinan zaben da ya baiyana sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa gabanin kammala tattara alkaluman sakamakon ta nemi sufetan 'yan sandan Najeriya ya gurfanar da shi a gaban kotu.

Bayan kamalla taron jiga jigan jami'anta INEC din ta nemi babban sufeton yan sanda na kasar da ya tabbatar da gurfanar da kwamishinan zabe na jihar Hudu Ari. A wata wasikar da INEC din ta aike wa sufeton yan sandan na kasa, a fadar mai magana da yawun hukumar Zainab Aminu ta ce akwai bukatar hukunta kwamishinan zaben Hudu Ari.

Tuni dai wata tawagar manyan kwamishinonin hukumar zaben ta kasa suka isa Yola hedikwatar jihar Adamawan a karkashin jagorancin Festus Okoye a wani abun da ke nuni da rushe sanarwar Hudu Arin. Wata kara da 'yar takarar ta jam'iyyar APC ta shigar a Abuja da nufin neman tsayuwar gwamen jaki bisa sakamakon dai ta gaza kaiwa ya zuwa samun tagomashin alkalan na Abuja.

Mai shari'a Inyang Okoro na babbar kotun da ke a Abuja ta nemi lauyoyin Binani su tabbatar da batun hurumin sauraron karar kafin sanin mataki na gaba. Ana dai kallon jerin kiki kakar Adamawar da idon barazana ga makomar tsarin dimukuradiyyar Najeriyar da ke dada neman wurin zama.

Kuma a fadar Faruok BB Farouk mai sharhi kan al'amuran siyasa, sanya son rai a ayyukan hukumar zaben ne ke neman jawo matsala ga makomar tsarin zaben kasar. To sai dai kuma a tunanin farfesa Almustapha Osuji da ke zaman kwarare bisa kundin tsarin mulki abun da ke faruwa a jihar Adamawar bai saba da kaidojin dokar kasar ba.