Firaministar Italiya Meloni ta gana Trump kan yakin Ukraine
January 5, 2025Firaministar Italiya Giorgia Meloni ta gana da shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump a gidan hutawarsa na Mar-a-Lago da ke birnin Florida, gabanin bikin rantsar da shi a kan karagar mulkin kasar ranar 20 ga wannan wata na Janairu, da nufin kara karfafa alaka tsakanin Italiya da Amurka.
karin bayani:Firaministar Italiya Giorgia Meloni ta kaddamar da bikin taron kasarta da shugabannin Afirka
Ko da yake ba a kai ga fitar da bayanin dukkan abubuwan da shugabannin biyu suka tattauna a kai ba, to amma Meloni ta bukaci ganawar tun asali da Trump da ke zama abokin 'dasawarta, don tattaunawa kan yakin Ukraine da Rasha, da rikicin Gabas ta Tsakiya, sai halin da 'yar jaridar Italiya da gwamnatin Iran ta kama ke ciki, sannan kuma da batun sha'anin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.
Karin bayani:Sarki Charles na Burtaniya ya jinjinawa al'ummar kasar Ukraine bisa juriyar yaki da Rasha
Nan gaba ne kuma Firaministar ta Italiya Giorgia Meloni za ta gana da shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden, to amma ofishinta bai bayar da wani karin bayanin ko me za su tattauna a kai ba.