SiyasaTurai
Sarki Charles ya jinjinawa al'ummar Ukraine a kan Rasha
February 24, 2024Talla
Sarki Charles na III na Burtaniya ya jinjinawa al'ummar kasar Ukraine bisa juriyar da suke nunawa a daidai wannan lokaci da kasarsu ke cika shekaru biyu da fuskantar mamaya daga sojojin Rasha.
Karin bayani:Duniya na fatan alkahiri ga Sarki Charles
Sarki Charles ya jaddada cewa hakika sun cancanci yabo a cikin wannan mummunan yanayi na ba gaira ba dalilin afka musu.
Karin bayani:An nada Sarkin Ingila bayan shekaru 70
Tuni dai manyan shugabannin kasashen duniya suka isa birnin Kiev don taya Ukraine jimamin halin da ta samu kanta a ciki. Wadanda suka hada da shugabar kungiyar tarayyar Turai EU Ursula von del Leyen, firaministan Belgium Alexander de Croo, Sai firaministar Italiya kuma mai rikon mukamin shugabancin kasashen G7 Giogia Meloni.