1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakile COVID-19 a Gabas ta Tsakiya

Mahmud Yaya Azare LMJ
March 23, 2020

A kokarinsu na dakile yaduwar annobar cutar Coronavirus da ke ci gaba da mamayar kasashen duniya, mahukunta a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya sun dauki matakan ba sani ba sabo na tunkarar cutar.

https://p.dw.com/p/3ZvHO
Coronavirus SARS-CoV-2 im Elektronenmikroskop
Duniya na fuskantar barazana daga COVID-19Hoto: picture-alliance/AP/NIAID-RML

Firaministan hukumar Falalsdinawa Muhammad Ashteyah ya sanar da dokar hana bulaguro tsakanin jihohi da garuruwa da ma cikin garuruwan tun daga almuru a fadin Falalsdinu, bayan da mutane shida suka kamu da cutar a kasar, matakin da kasashe da dama a yankin suka dauki makamancinsa koma mafi tsanani. A kasar Lebanan inda mutane 209 suka kamu da cutar ta Coronavirus ko COVID-19, dakarun sojojin kasar sun yi amfani da karfi wajen hana fita da yin gargadin hukunta duk wanda ya sabawa wannan dokar. 

Saudi-Arabien Die Kaaba wird desinfiziert
Feshin magani a Ka'abaHoto: picture-alliance/dpa/A. Nabil

A Saudiya ma an saka dokar hana yawon dare ne, a yayin da ita kuwa masarautar Hadaddiyar Daular Larabawa ta bakin mukaddashin ministan lafiyar kasar Faridah Al-Hausabi  ta nemi al'umma da su guji wasu al'adu da za su iya kara ta'azzara yaduwar cutar.

Mutane na kokarin bin umurni

A Masar kuwa rundunar sojin kasar ta bayar da sanarwar mutuwar wani babban janar din soja, bayan da ya kamu da cutar ta corona a yayin da yake jagorantar rundunar kar ta kwana domin aiwatar da umarnin hana zirg-zirga da yin feshin tsaftace tituna da manyan wuraren taruwar jama'a. A nasa bangaren Shugaba Abdulfattah Alsisi ya gargadi al'ummar kasar kan cewa wannan annoba ka iya zama bala'i muddin  za su ci gaba da yin ko oho ko kuma izgilanci ga umarnin ma'aikatan lafiya. 

Tuni dai mutane suka shiga taitayinsu a galibin kasashen yankin Gabas ta Tsakiyar, kama daga killace kai da yawo da marfun fuska da hanci gami da kwalbar sinadarin tsaftace hannu. Wani dattijo da ya yi shekaru 30 yana tukin Taxi ya bayyana irin sabon matakin da ya dauka, inda ya ce duk safiya idan ya fito da motarsa, sai ya yi mata feshi a ciki da wajenta, kana ya kan kuma tanadi marafan baki da hanci domin bai wa fasinjan da ya dauka a matsayin kariya.