Nijar: Dage karbar kasafin kudin badi
September 28, 2020Kasafin kudin na Nijar na shekara mai kamawa wanda gwamnatin ta gabatar gaban kwamitin majalisar kafin ranar da minista zai bayyana a zauran majalisar, ya kai sama da biliyan dubu biyu da 500 na kudin Cefa wato karin kusan biliyan 200 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata. Tun dai hawan mulkin Shugaba Mahamadou Issoufou ne, kasafin kudin Jamhuriyar ta Nijar ke karuwa a kowace shekara, kuma a fadar Honnorable Iro Sani na jam'iyyar PNDS Tarayyar hakan wata alama ce da ke nuni da irin ci-gaban da Nijar ke samu a karkashin mulkin nasu.
Karin Bayani: Nijar: Hama Amadou zai tsaya takara
To sai dai, da yake mayar da martani kan alfaharin da masu mulkin ke yi kan karuwar kasafin kudin kasa a kowace shekara, Honourable Soumana Sanda na jam'iyyar adawa ta Lumana Afirka, cewa ya yi babu wani ci-gaban da Nijar ke gani a kasa sakamakon karuwar kasafin kudin.
A wannan Litinin din ya kamata ministan kudi na Nijar ya bayyana a gaban kwamitin majalisa domin gabatar da kasasfin kudin badin, kafin zuwa ranar muhawara a zauran majalisar.
Karin Bayani: Shirin zabe da rudanin siyasa a Nijar
To sai dai kuma gwamnati ta bukaci a dage zaman domin yin gyaran fuska ga kasafin kudin kasa na shekarar bana. Abin kuma da Honnorable Sumana Sanda na jam'iyyar adawa ta Lumana Afirka, ya ce, hakan ya kara tabbatar da maganar da suke na cewa kasafin kudin na saman takarda ne kawai. To sai dai Honnorable Iro sani na jam'iyyar PNDS Tarayyar, ya ce akwai dalili mai karfi da ya sa gwamnatin ta dakatar da zaman mika kasafin kudin na bana domin yi masa kwaskwarima. Bayan da gwamnatin ta dage zaman majalisar da za ta yi kan nazarin kasafin kudin na shekarar badi dai, 'yan majalisar sun kasa kunne suna sauraron ranar da ministan kudin zai bayyana a gabansu, domin gabatar da sabon kasafin kudin da kuma bayar da bahasi a kai.