1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudani a babban zaben kasar Gabon

August 9, 2023

Cece-kuce ya barke tsakanin 'yan siyasar Gabon, sakamakon matakin da Hukumar Zabe ta dauka na tanadar kuri'a daya tilo ga kowanne dan kasa a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa.

https://p.dw.com/p/4UxhB
Gabon | Ali Bongo Ondimba | Siyasa | Zabe
Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba Hoto: ISABEL INFANTES/AFP

Wasu 'yan adawar kasar Gabon sun zargi gwamnati da hana mutane zabar jam'iyyu biyu mabambanta a tagwayen zabukan, lamarin da ya haddasa rudani, makonni uku gabanin babban zaben. 'Yan takarar da jam'iyyun siyasar Gabon suka tsayar dai, na ci gaba da zagawa sako da lungu na kasar domin tallata manufofinsu. Sai dai a daidai lokacin da fagen siyasa na kasar da ke yankin Tsakiyar Afirka ke daukar harami, garambawul da aka yi wa kundin kada kuri'a na tayar da jijiyoyin wuya. Al'ummar Gabon dai sun kasa fahimtar dalilin da ya sa hukumar yanke wannan shawarar a kurarren lokaci. A nata bangaren Hukumar Zaben ta danganta wannan sabon matakin da hanyar da ya kamata a bi, domin saukaka tsarin zabe. A yayin taron manema labarai da ya shirya a Libreville babban birnin kasar, shugaban Hukumar Zaben ta GCE Michel Bonda ya ce hakan zai magance korafe-korafen rashin gane 'yan takara da wadanda ba su yi karatu ba ke yi. A cewarsa duk wanda ya zabi dan takarar shugaban kasa na wata jam'iyya, tamkar ya zabi dan takarar majalisa da wannan jam'iyyar ta tsayar a mazabarsa ne kai tsaye.

Gabon | Libreville | Majalisar Dokoki | Zabuka
Zauren majalisar dokokin GabonHoto: Wils Yanick Maniengui/AFP/Getty Images

Sai dai 'yan adawa ba su yi wata-wata ba wajen mayar da zazzafan martani, inda gamayyar jam'iyyu ta Alternance 2023 wacce ta hada jam'iyyun adawa da dama ta yi tir da matakin tanadar wannan kuri'a daya tilo a tagwayen zabukan na Gabon. A gare ta dai, wannan kwaskwarima ga kundin kada kuri'ar a Gabon ta haifar da rudani tare da nuna wariya ga 'yan takara masu zaman kansu tare da bukatar a mutunta 'yancin kowa na zaben shugaban kasa da 'ydan majalisa da ya kwanta masa kamar yadda tsarin dimukuradiyya ya tanadar. Ta kuma yi kira da a soke tsarin katin kada kuri'a daya da kuma amfani da akwatunan zabe dabam-dabam ga kowane katin zabe. A yanzu dai, ayoyon tambaya sun dabaibaye zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a Gabon. Wai shin zai yiwu a zabi 'yan takara na shugaban kasa da na 'yan majalisa daga jam'iyyu dabam-dabam a kowane zabe? Ya dan kasa zai zabi dan majalisarsa idan ya zabi dan takara mai zaman kansa a zaben 'yan majalisa? Sai dai kash, wadannan tambayoyi ba su samu amsa daga Hukumar Zabe ba tukuna. A ranar 26 ga watan Agusta ne dai, za a gudanar da wadannan tagwayen zabukan na Gabon.