Ganawar Cif Obasanjo da Shugaba Jonathan
August 28, 2014Dangantaka tsakanin Cif Olusegun Obasanjo da Shugaba Goodluck Jonathan ta yi tsami a 'yan shekarun da suka gabata wanda hakan ya biyo bayan maganganun da Cif Obasanjo ya yi na cewar Shugaba Jonathan din baya tafiyar da mulkin kasar yadda ya kamata, batun da bai yi wa fadar shugaban kasar dadi ba. Wannan batu ne ma ake kallo a mastsayin musababbin tsamin dangantakarsu.
To sai dai duk da tsamin dangantakar da ke akwai tsakaninsu, Cif Obasanjo ya yi takakkiya zuwa fadar mulki ta Aso Rock da ke Abuja inda ya gana da shugaban kasar wanda hakan ya jefa fata na sake komawa danyane ganye da ka iya yin tasiri wajen kawo saukin matsalar tsaron da kasar ke fuskanta musamman sanin matsayin Cif Obasanjo a Najeriyar da ma kasashen Afrika.
Tuni dai al'ummar kasar irin su Dr. Sadeeq Abba da ke zaman masanin kimiyyar siyasa a jami'ar Abuja suka fara tofa albarkacin bakinsu dangane da tasirin da tsoma bakin Obasanjo zai yi wajen kaiwa ga warware matsalar inda ya ke cewa kyautuwa ya yi a ce shugabannin biyu sun yi ganawar tun tuni don shawo kan wannan matsalar kafin ta kai haka dagulewa.
Shi kuwa Barr. Mainasara Umar da ke sharhi kan al'amuran yau da kullum a kasar ya ce akwai bukatar taka tsantsan da irin wannan zantawa da bangarorin biyu suka yi domin kuwa kowa ya san siyasa ce ta hada su saboda haka ya kamata a yi hattara don gudun yin kitso da kwarkwata duba da yanayin da ake ciki yanzu haka.
To sai dai yayin da masharhanta ke tofa albarkacin bakunansu dangane da wannan zantawa da Cif Obasanjo yai da Shugaba Jonathan, wani bangare na al'ummar kasar na jinjina dalilan da ya sanya sauran tsofafin shugabanin Najeriyar suka yi shiru game da wannan matsala, yayin da wasu ke zuba idanu don ganin tasirin da yunkurin na Obasanjo zai yi wajen shawo kan kalubalen da kasar fuskanta a bangaren tsaro.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Ahmed Salisu/AH