Najeriya: Kudiri kan gyaran fuska ga dokar zabe
July 16, 2021A Najeriya hukumar kula da kafofin sadarwa ta kasar, ta shaidawa ‘yan majalisar wakilai cewa hukumar zaben Najeriyar ba za ta iya aikawa da sakamakon zabe ta amfani da yanar gizo daga dukkanin rumfunan zaben kasar ba, a yayin da 'yan jamiyyar PDP suka fice daga zauren majalisar a fusace.
Karin Bayani: Mafita kan makomar zaben 2023 a Najeriya
Hukumar kula da kafofin yada labarun Najeriya NCC ta zama raba gardama a kan kiki-kan da aka fuskanta a majalisar wakilan Najeriyar kan gyaran fuska ga dokar zaben Najeriyar da ake son amfani da yanar gizo wajen aikewa da sakamakon zabe a 2023.
Ta dai kai ga dambacewa a tsakanin ‘yan majalisar abin da ya sanya gayyato hukumar ta NCC don warware zare da abawa. Jami’ai har hudu ne karkashin jagorancin Ubale Ahmed suka shaidawa majalisar cewa babu yadda za’a yi hukumar zabe ta iya tura sakamakon ta yanar gizo, domin rabin mazabun Najeriyar ne ke da hanyar waya ta 2G da 3G, kuma sai da 3g ne za’a iya aikawa da sakamakon zabe. Nan ne hatsaniyar ta kaure a tsakanin ‘yan majalisar.
Karin Bayani: Rudani ga babban zaben Najeriya na 2015 Hanarabel Elumelu Ndudi shi ne shugaban marasa rinjaye a majalisar, ya ce, alkawari aka yi na gayyato hukumar zabe da ta NCC don haka an yi masu coge a daukacin al’amarin.
‘Yayan jamiyyar PDP da suke da ja a kan wannan al’amari, sun kai ga fusata da ma ficewa daga zauren majalisar a dai dai lokacin da ake muhawara ta amincewa da wannan sashi, wanda majalisar wakilan ta tsaya a kan bayanin da ta ce gamsashe ne a gareta, ba bu batun aikewa da sakamakon zabe ta yanar gizo.
Karin Bayani: Najeriya: INEC ta magantu kan Zamfara
Zargi na kaucewa dokokin majalisa da akewa shugabaninta a wannan lamari da ya sanya hargitsa lamura duka a kokari na kai wa ga madafan iko a kan batun zabe a Najeriyar musamman zaben 2023 muhimi. A yanzu dai majalisar wakilan Najeriyar ta bi sahun ta dattawa wajen cimma matsaya a kan wannan batu na aikewa da sakamakon zabe, ta hanyar amfani da yanar gizo wanda shi ne yafi daukan hankali a daukacin gayran fuskar da aka yi wa dokokin zaben Najeriya, a kokari na kyautata tsarin zabe a kasar da ya sanya jan layi tsakanin jamiyyar APC mai mulki da ta ‘yan adawa.