1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniAsiya

Masu neman mafaka na gasar cin kofin kwallon kafa

Abdoulaye Mamane Amadou LM
September 26, 2024

Shekaru biyu bayan dakatar da ita saboda bullar annobar Corona, gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da masu neman mafaka da ba su da muhalli ke buga wa na ci gaba da gudana a birnin Seoul na kasar Koriya ta Kudu.

https://p.dw.com/p/4l7jM
Koriya ta Kudu l Gasa | Kwallon Kafa | Masu Neman Mafaka
Gasar cin kofin kwallon kafa ta masu neman mafaka a Koriya ta KuduHoto: Jung Yeon-Je/AFP

Gasar da a karon farko ke samun tallafin Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA, na gudana ne ba tare da wata tangarda ba a birnin na Seoul. Kowace tawaga, za ta share mintuna 14 tana kece raini da wacce suke fafatawa a tsakiyar fili. Masu neman mafaka, wadanda suka kasa samun muhalli da 'yan gudun hijra kamar su Fossi Wandji zalla ne ke barje guminsu a wasan. Wandji dan asalin kasar Kamaru da ya shiga Koriya ta Kudu shekaru biyun da suka gaba a matsayin dan gudun hijira, manufarsa ita ce tsirar da kansa daga yakin basasar da ya daidaita yankin da ke amfani da harshen Turancin Ingilishi a Kamarun. Mai shekaru 27 a duniyar na a matsayin bakar fata tilo da ke buga wasa a tawagar 'yan Koriya ta Kudu, kuma kasar ce ta ba shi wannan dama duk da yake yana dakon hukumomi su ba shi mafaka. A shekara ta 2022 matashin ya tsallaka daga Kamaru, an dakatar da shi a filin jiragen saman Koriya ta Kudun.

Koriya ta Kudu | Fossi Wandji  l Kamaru | Mafaka
Dan wasan Kamaru mai neman mafaka a Koriya ta Kudu Fossi Wandji Hoto: Jung Yeon-Je/AFP

Ya yi ta kokarin bambanta kansa da sauran 'yan gudun hijira domin samar wa kansa mafita, sai dai har yanzu yana dakon mataki na gaba da kotu za ta yanke kan makomarsa a kasar ta Koriya. Burinsa shi ne ya haska a gasar ta wannan karon, ko abin zai zo masa da sauki. Gasar marasa muhllin da 'yan gudun hijira an fara ta ne a shekara ta 2003 a kasar Austria, wasu abokan juna biyu Mail da Herrent ne suka assasata da nufin bai wa mutanen da ke cikin yanayi na rashin matsuguni wata dama. Tun daga wancan lokacin gasar ke taka muhimiyar rawa, kana tana da matukar tasiri har ma a Najeriya in ji Anas Ba Musa Kwame mai fashin baki kan harkokin wasanni a kasar. Ya kuma kara da cewa duba da matsalar da ake samu a fannin rashin muhalli a duniya, nahiyar Afirka na cin gagarumar moriyar gasar. A ranar 28 ga wannan wata na Satumba da muke ciki ne za a kawo kashen gasar cin kofin na duniya, inda dimbin 'yan gudun hijira da ke neman mafaka kamar su Fossi daga Kamaru ke fatan samun sa'ida ta hanyar gasar.