Iran: rikicin Gaza ya yadu a yankin Larabawa
November 10, 2023A yayin wata hira ta wayar tarho jami'in diflomasiyyan na Teheran Hossein Amir-Abdollahian ya shaida wa takwaransa na Qatar Mohammed ben Abdelrahmane Al-Thani cewa la'akari da yadda yakin ke ci gaba da haddasa asarar rayukan fararen hula mazauna Gaza ya zama wajibi rikicin ya fadada a fadin yankin.
Karin bayani: Shugaban Amurka Joe Biden ya ce babu yiwuwar tsagaita wuta a Gaza.Biden
Akalla mutane 1,400 ne suka halaka a Isra'ila tun bayan da kungiyar Hamas mai iko da zirin Gaza ta kai harin ba zata wanda ba a taba ganin irinsa ba, yayin da a bangaren Falasdinu aka sanar da mutuwar fararen hula akalla 10,812 ciki har da kananan yara 4,412.
Karin Bayani: Turkiyya ta bukaci Amurka ta sa baki don tsagaita wuta a Gaza
To sai dai yayin da ake wannan fargaba Amurka da ke zama babbar kawar Isra'ila ta aike da jiragen yaki i zuwa Gabashin Tekun Mediteranean da nufin bai wa Isra'ila kariya da kuma dakatar da duk wani yunkuri na fadadar rikicin.