Gaza: Isra'ila ta zafafa kai hare-hare
March 28, 2024Fadan ya fi kamari ne a Khan Younis da ke kudancin Gaza, sannan kamfanin dillacin labaran Falasdinu na Wafa ya bayar da rahoton dauki ba dadi a wasu garuruwa na yankin gabar yamma da kogin Jordan.
Da sanyin safiyar Alhamis ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ba da rahoton mutuwar akalla mutane 66 sakamakon hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai a cikin dare, galibi a asibitoci inda suke zargin mayakan Hamas sun nemi mafaka.
A gefe guda kasar Qatar da ke shiga tsakani a rikicin tare da Masar da Amurka sun ce suna ci gaba da tattaunawa da nufin samar da tsagaita wuta na makonni tare kuma da musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas.
Karin bayani: Gaza: Isra'ila ta dage kan afkawa Rafah
Kazalika ita ma Isra'ila ta sanar da sake bude kofar tattaunawa da Amurka, bayan da ta ki halartar zaman farko da aka shirya domin nuna fushi ga matakin Washington na kaurace wa kuri'ar zartar da kudirin tsagaita wuta da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi a wannan mako.