Girgizar kasa ta kashe mutane sama da 100 a Nepal
November 4, 2023Lamarin ya auku ne a daren jiya Juma'a, wanda kuma ya yi sanadiyyar rayukan mutane sama da 132 a cewar sanarwar da hukumomi suka fidda.
An sami asarar rushewar gidaje da dama, tuni masu aikin ceto suka fara kokarin zakulo mutanen da ke da saurin numfashi da suka makale a baraguzan gini.
Hukumomin lafiya sun ce sama da mutane 100 ne suka sami munanann raunika kuma yanzu haka ke karbar kulawa likitoci a asibiti.
Kasar Indiya da ke da nisan kilomita 500 daga inda wannan ibtila'in ya auku ta sanar da jiyo girgizar kasar.
A shekarar 2015, mummunar girgizar kasa mai karfin maki 7.8 ta auku a kasar Nepal inda aka yi asarar rayukan mutane sama da 22,000, inda al'umma suka shiga wani mawuyacin hali.
Karin bayani: Ana fuskantar gwagwarmayar raba kayan agaji bayan girgizar kasa a Nepal