1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Mali na shirin karbe madafan ikon kasar

September 22, 2023

Jagoran mulkin sojin Mali Kanar Assimi Goita ya yi alkawarin sake kwace ikon kasar da ke fama da tashe-tashen hankula daga kungiyoyin masu da'awar jihadi da 'yan tawaye.

https://p.dw.com/p/4WiGt
Assimi GoïtaHoto: Präsidentschaft der Republik Mali

Da yake magana a kan bikin cikar kasar ta  Afirka ta Yamma shekaru 63 da samun 'yancin kai daga Faransa, Goitaya yi amanar cewa gwamnatinsa na fuskantar babban kalubale.

Tun a shekara ta 2012 ne dai rikicin 'yan tawaye ya barke a arewacin Mali, wanda ya bazu zuwa Nijar da Burkina Faso da ke makwabtaka. Kasar ta Mali ta fuskanci juyin mulki a kai a kai tsakanin shekarar 2020 da 2021, kuma mafi yawancin kasar ba ya karkarkashin ikon gwamnati.

Mayakan jihadi na ci gaba da fadada madafan ikonsu a yankunan karkara a arewacin kasar,  inda a ranar Alhamis suka kai hari kan birnin Timbuktu.

A bara ne dai, sojojin Mali suka fatattaki dakarun Faransa masu yaki da 'yan tawayen da kuma tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin DuniyaMINUSMA a wannan shekarar 2023 da mu ke ciki.