Kwashe ragowar dakarun Minusma zai kasance da wuya
August 28, 2023Shugaban rundunar Minusma a Mali El Ghassim Wane ya tabbatar da cewa duk da yake an kusa martaba wa'adin da gwamnatin Mali ta dibar wa dakarun na ficewa daga kasar kafin karshen wannan shekara, akwai rashin tabbas ga ragowar sansanonin duba da tsaikon da aka samu bayan rufe sansanin Ber da ke Arewa maso gabashin Mali.
Karin Bayani : An kai wa dakarun MINUSMA hari a Mali
El Ghassim Wane ya kara da cewa juyin mulkin Nijar a karshen watan jiya, ya kara dagula lamurran kammala kwashe dakarun na Minusma, duba da yadda sojojin rundunar ke tsanain bukatar bi a Nijar kafin tsallakawa zuwa gabar tekun Cotonou na kasar Jamhuriyar Benin ko Lome na kasar Togo.
Karin bayani : Mali: Kawo karshen aikin rundunar MINUSMA
Gwamnatin Bamako ta bai wa Majalisar Dinkin Duniya wa'adin 31 ga watan Disamaban wannan shekara da ta kwashe nata-ya-nata ta bar kasar, sai dai har yanzu sansanoni hudu ne kawai suka fice, daga cikin 10 da dakarunta na Minusma ke amfani da su a Mali.