1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLibiya

Guguwa da ambaliya sun kashe rayuka a Libiya

September 12, 2023

Rahotanni daga kasar Libiya na cewa daruruwan mutane ne wani sabon ibtila'in ruwan sama ya shafa. Lamarin da ya auku a gabashin kasar ya yi kisa wasu ma sun bata.

https://p.dw.com/p/4WEE7
Hoto: AA/picture alliance

Akalla mutane 150 ne hukumomi a Libiya suka tabbatar da mutuwarsu, sakamakon ibtila'in ambaliyar ruwa  da ya afka wa yakin gabashin kasar.

Wasu hotunan bidiyo da mazauna yankunan da abin ya shafa suka yada, sun nuna yadda gine-gine ke ta zaftarewa suna fadawa a kan jama'a bayan ruwa ya malale ko'ina.

Wannan na kuma zuwa ne bayan wata guguwa hade da ruwan sama mai lakabin Daniel da ta shafi tekun Bahar Rum, ta yi wani ta'adin a kasashe Turkiyya da Bulgaria da ma kasar Girka.

A wani bayanin da ya yi ta kafar talabijin din Al Masar Network, Firaministan gwamnatin gabashin Libiyar, Oussama Hamad, ya ce daruruwan mutane ne suka mutu, yayin kuma da wasu dubban suka bata.