Najeriya: Gargadi a kan ambaliya
August 28, 2023Hukumar ta ba da agajin na gaggawa ta NEMA ta fidda sanarwar cewar ,Kasar ta Kamaru za ta sako ruwan wannan Dam na LAGDAM da ke neman haifar musu da barna a kasar. Sakamakon mamakon ruwan sama, kuma da jin haka ne, hukumar ta NEMA a cikin sanarwar da ta bayyana ta ce dole a fara daukar matakan gaggawa na fara fadakar da jama'ar; da ake hasashen wannan ballo ruwan na LAGDAM zai yi wa barna, ta fara zakudar da su, musamman ma ganin ruwan zai biyo ne ta turbar kogin River Niger. Sanarwa kumama ta nunar jahohin da ke makwabtar wannan kogi irin su Anambara da Bayelsa da Rivers da kuma Cross River, gami da Edo, yanzu zaa fara zakudar da jama'ar su da a ka tabbatar gararin ballo ruwan zai shafa.
Ambaliyar za ta iya shafar yankunan kudancin Najeriyar da dama
Ruwan dai an tabbatar in har a ka ballo shi, to kuwa zai yi awon gaba da duk wani gini ko dai makamancin haka da ke kan hanyar sa. Tuni dai hukumar ta NEMA ta ce ta sanar da jahohin 11 a kasar, da al'amarin ya shafa. To ganin dai a ranar 14 ga watan gobe na Augusta Kamaru din za ta sako wannan ruwa, na ji ta bakin wani dan jahar Bayelsa, da gararin ambaliyar ruwan bara ta tagayyara, mai suna Kakiri Nwangidibamu wanda ya ce babbar barazana ce. Kawo yanzu dai al'ummomi da dama da al'amarin ka iya shafa, sun fara tunanin zakudawa kan tuddai ,don kaucewa daga gararin na ballowar wannan ruwa. Ambaliyar ruwan bara dai ta kassara yawan jama'ar da ta kai miliyan 1.4. sannan mutane 603 sun mutu,mutane kuma 2400 sun jikkata,haka kuma gidaje 82,035 sun rurrushe, sannan ya yi barna ga fadin Hekta ta kasa 332,327.