1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yajin aikin kungiyar ASUU

Uwais Abubakar Idris
November 5, 2018

A Najeriya, kungiyar malaman jami'o'in kasar ta tsunduma cikin yajin aiki a dai dai lokacin da ita ma kungiyar kwadago ta ce ba ja da baya a nata yajin da take shirin dakawa.

https://p.dw.com/p/37fxw
Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Wannan batu na yajin aiki dai ya jefa damuwa a kan illar da hakan ke tattare da shi ga kasar da al'ummarta. Kungiyar Malaman jami'o'in Najeriyar dai ta danganata dalilanta na tsunduma cikin yajin aikin da suka hadar da rashin samar da isassun kudin gudanarwa ga jami'o'in kasar da ta ce na kawo cikas ga daukacin harkokin ilimi. Kama daga rashin kayan koyarwa ya zuwa na bincike ko nazari da ma yanayin da zai taimaka gudanar da binciken, abin da ya sanya shugaban kungiyar Farfesa Abiodun Ogunyemi ya umurci daukacin 'ya'yan kungiyar da su tsunduma cikin yajin aikin.

Rashin cika alkawari daga gwamnati

Protestierende Studenten während ASUU Streik in Kano
Yajin aikin kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUUHoto: DW/N. S. Zango

Fiye da shekara guda kenan da kungiyar malaman jami'o'in Najeriyar ta dakatar da yajin aikin da ta yi a shekarar da ta gabata, a lokacin da ta ce dama ta dakatar da yajin aikin ne domin ganin ko gwamnatin za ta cika mata alkawarinta. Yawan yaje-yajen aiki ga malaman jami'o'in Najeriyar dai, lamari ne da ake nuna damuwa da illar da zai yi. A dai dai lokacin da kungiyar malaman jami'o'in ke yajin aikin, ita ma kungiyar kwadagon Najeriyar na tattara nata komatsan domin shiga yajin aikin. To sai dai gwamnatin kasar ta samo umurnin kotu da ya haramtawa kungiyar daukar wannan mataki. Al'ummar Najeriyar dai na nuna damuwa kan halin da za a iya shiga a kasar dalilin yajin aikin da ka iya durkusara da daukacin al'amura a kasar, a wannan lokaci mai muhimmancin gaske. Za a sa ido a ga ko gwamnatin za ta shawo kan ma'aikatan ganin sun kauracewa tattaunawar da ya kamata su yi a karshen mako.