1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Tasirin karin albashi ga tattalin arziki

Uwais Abubakar Idris
November 6, 2018

A Najeriya ma’aikatan kasar sun fara maida murtani a game da cimma yarjejeinya ta karin albashi da suka dade suna nema, biyo bayan amincewa da hakan a tattaunawa tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin Najeriyar

https://p.dw.com/p/37k1t
Nigeria Geld Geldscheine Naira in Lagos
Hoto: Getty Images

An dai kai ga cimma wannan matsaya ne bayan fito na fito da ma barazanar shiga yajin aiki da gamaiyar kungiyoyin kwadagon Najeriyar suka yi ga gwamnatin kasa. Daga karshe dai gwamnatin ta amince da bukatun kungiyar na lallai sai dai a karawa ma'aikatan albashi mafi kankanta daga Naira dubu 18 zuwa Naira  dubu 30 da suka dage a kansa.

Duk da cewa za'a gabatarwa shugaban kasa da wannan matsaya da aka cimawa da maraicen talatar nan. Ko me suka amince da shi ne ya sanya su dakatar da yajin aikin da suke cewa a kowane lokaci zasu iya kara daka abinsu su sha.

Tuni dai ma'aikatan gwamnatin a Najeriyar suka shiga doki da murna a kan wannan karin albashi da aka yi masu, sanin cewa sun dade suna kukan cewa abinda suke karba  baya isarsu.

A yayinda ma'aikatan ke murna da jiran cikakken bayani na lokacin da zasu fara cika aljihunsu da sabon albashi bayan shekaru tara da aka yi karin, masana tattalin arziki na masu bayyana cewa matsalar ma'aikata ban a karin albashi bane.

A daidai lokacin da ma'aikata ke sa idon lokacin da zasu fara cika aljihunansu da sabon albashi ana ci gaba da nazarin tasirin da zai yi ta fanin rayuwar sauran ‘yan Najeriya sanin cewa daukacin ma'aikatan gwamnati basu kai milyan daya ba daga kusan mutanen milyan 200 da ke Najeriyar.