1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnati ta dakile yunkurin hargitsa Burkia Faso

Abdoulaye Mamane Amadou Babayo
September 24, 2024

Gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ta zargi hannun kasashen ketare wajen yunkurin tayar mata da hargitsi a cikin kasa

https://p.dw.com/p/4l09Q
Burkina Faso | Übergangspräsident Ibrahim Traore
Hoto: Donat Sorokin/TASS/dpa/picture alliance

Majalisar mulkin soja ta rikon kwarya a Burkina Faso ta zargi tshon shugaban mulkin soji kasar da ta kora Paul Henri Sandaogo Damiba, da hannu wajen yunkurin tada zaune tsaye da hargitsa kasar

Karin bayani :Mali da Nijar da Burkina Faso za su kaddamar da sabon fasfo

A cikin wata sanarwar da ta fitar a wannan Litinin, Ouagadougou ta zargi wasu manyan kasasshen duniya da hannu wajen yunkurin hadasa fitina ta hanyar tallafawa korarren shugaban kasar na mulkin soja Kanar Damiba da yanzu hakan ke samun mafaka a kasar Togo.

Karin bayani : Shekara da kafa AES

Ma'aikatar cikin gidan kasar ta sanar da kama wasu mutane da dama ciki har da hafsosshin soja da ta zarga kai tsaye da yunkurin. Kana ma'aikatar cikin gidan ta Burkina Faso ta kuma bayyana sunan dan jaridar nan na Nijar dan asalin kasar Côte d'Ivoire da ya yi batan dabo Serge Maturin Adou da hannu cikin lamarin.