Mali da Nijar da Burkina Faso za su kaddamar da sabon fasfo
September 16, 2024Nan ba da jimawa ba kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso za su kaddamar da sabon fasfo domin saukake tafiye-tafiye tsakaninsu.
Shugaban gwamnatin mulkin sojin Mali Kanal Assimi Goita ne ya fadi haka a yayin da kasashen ke neman karfafa dangantaka tsakaninsu bayan ficewa daga kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS.
Mali da Nijar da Burkina sun juya wa ECOWAS baya
Kasashen uku da ke karkashin mulkin soji sun kafa kungiyarsu ta AES a watan Satumban 2023 bayan raba gari da uwargijiyarsu Faransa da kuma karkata ga Rasha.
A wani jawabi da ya gabatar, Kanal Goita ya ce nan da 'yan kwanaki sabon fasfo din na kasashen AES zai fara zagayawa da manufar saukaka tafiye-tafiye tsakanin kasashen.
Shugaban Senegal zai sasanta ECOWAS da AES
Wannan sanarwar na zuwa ne kwana guda kafun cikar kawancen na AES shekara daya da kafuwa.