1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabon

Gwamnatin mulkin sojan Gabon ta nada majalisa

October 7, 2023

Gwamnatin rikon kwaryar Gabon ta yi nadin sabuwar majalisa sai dai ba tare da ta sanar da lokacin da ta mika mulki ga farar hula ba.

https://p.dw.com/p/4XF5n
Gwamnatin mulkin sojan Gabon ta nada majalisaHoto: AFP/Getty Images

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Gabon janar Brice Oligui Nguema ya nada sabbin 'yan majalisar dokokin da kuma sanatoci a ranar Asabar (07.10.2023) domin shinfida sabuwar tafiya wa mutanen wannan karamar kasa mai arzikin man fetur da ke Tsakiyar Afrika.

Karin bayani: Sojoji a Gabon sun ce ba za su yi hanzarin gudanar da zabe ba

Sabuwar majalisar dokokin ta kunshi mambobi 98 da kuma sanatoci 70 da suka fito daga jam'iyyu siyasa na adawa da na hambararriyar gwamnati da kuma kungiyoyi daban-daban da suka hadar da na kwadago da 'yan farar hula da kuma sarakunan gargajiya da malaman addini.

Sai dai sabin 'yan majalisun da aka nada ba su da cikakken wakilci, domin nan zuwa gaba ne bayan wani zaman mahawara na koli za a zabi wasu 'yan majalisun masu cikakken iko wadanda za a ba wa alhakin yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska kamar yadda sojojin suka alkawarta yi.

Karin bayani: Yunkurin maido da tsarin mulki a Gabon

A daya gefe kuma, duk da ya jaddada aniyarsa ta mika mulki ga farar hula cikin hamzari, shugaban na Gabon bai sanar ba da lokacin da za su dauka suna mulkin rikon kwarya kafin a dawo da kasar kan tafarkin dimukuradiyya ba.