Najeriya: Babu tilas a shirin tsugunar da makiyaya
July 1, 2019Shirin na Ruga dai na da babban burin samar da wurare tare da gina ababen more rayuwa da zummar inganta sana’ar kiwo a wasu zabbabun wurare a cikin jihohin Najeriya. Kuma babban makasudinsa na zaman kai karshen kai kawon makiyayan da ake zargi da hannu a rikice-rikicen da ke lakume rayuka a cikin kasar a halin yanzu.
Akalla jihohi goma sha biyu ne dai suka aiyana aniyarsu ta taka rawa cikin shirin a karon farko. To sai dai kuma tun ba’a kai ga ko’ina ba aka fara nunin yatsa a tsakani na jihohin da ke zargin gwamnatin kasar da kokari na kwace gonaki da nufin dadadawa makiyayan. Al’ummar Jihohi irin Benuwe da ke yankin Arewa ta tsakiya da ma gwamnoni na daukacin jihohin Kudu maso gabas da naa yamma sun ce a kai kasuwa, shirin da acewarsu ke neman maida sana’ar kiwo hidima ta gwamnatin tarraya.
Ana dai kallo na siyasa cikin shirin da ke neman raba kan kasar tsakani na arewa dama kudu. Abun jira a gani dai, na zaman yadda take iya kayawa ga shirin da ke zaman dabarar karshe ga gwamnatin na kai karshen matsalar da ke zaman ruwan dare gama duniyar kasar a halin yanzu.