Najeriya: Siyasa da karatowar zabe
February 10, 2022Akwai tarin matsaloli da rikicin cikin gida da jam'iyyun siyasar kasar musamman manyan jam'iyyun wato APC mai mulki da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP ke fuskanta, matsalolin kuma da ake ganin za su iya janyo nakasu da koma baya ga jam'iyyun a yayin zabukan na 2023. A yanzu haka dai jam'iyyar APC mai mulki ta rantsar da shugabannin jam'iyyar a maatakin jihohi, sai dai ban da wasu jihohi biyu sakamkon rikicin cikin gidan.
Jihar Kano na daga cikin jihohin biyu da aka gaza rantsar da shugabannin jam'iyyar ta APC da ke rike da madafun iko a matakin kasa da kuma jihar, abin da ya sanya uwar jam'iyyar nada wani kwamiti domin sulhunta rikicin. Sai dai kuma har yanzu ana ganin akwai sauran rina a kaba, domin kuwa bangaren Sanata Malam Ibrahim Shekarau a Kanon ya nunar da cewa bai amince da kwamitin da aka bai wa gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje rikonsa ba ganin cewa da bangaren gwamnan ne suke rikici.
Abu na baya-bayan nan da ya dauki hankali a siyasar Najeriyar kuma shi ne, wani mataki da majalisar dokokin kasar ke shirin dauka na kayyade digiri a matsayin matakin karatu da duk wani mai son tsayawa takarar gwamna ko shugabancin kasar zai kai kafin ya samu wannan dama. Baya ga haka majalisar dokokin Najeriyar, ta fara tattauna batun kafa doka mai tsauri kan jami'an gwamnati da ke dibar kudi domin zuwa kasashen waje neman lafiyarsu da ma ta iyalansu. Da dama dai na ganin duka wadannan kudirorin doka biyu, 'yan majalisar sun fara tattaunawa a kansu ne domin ganin zabukan shekara ta 2023 na kara karatowa.