1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki bayan zaben Markel a matsayin shugaba a Jamus

Zainab Mohd AbubakarNovember 22, 2005

Mace ta farko a matsayin sabuwar shugabar gwamnati a Jamus ta fara aiki gadan gadan

https://p.dw.com/p/Bu40
Hoto: dpa

Ya zuwa yanzu dai tuni sabuwar shugabar gwamnatin ta Jamus, wato Angela Markel, data kasance mace ta farko a tsawon tarihin kasar ta fara aiki gadan gadan.A yayinda a hannu guda kuma shugabannin kasashen duniya keta aike da sakonni tayata murnar wannan sabon matsayi data haye.

A gobe laraba ne sabuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel zata fara taka kasashen ketare cikin siyasar duniya a matsayin jagorar gwammnatin wannan kasa datafi kowace karfin tattalin arziki a nahiyar turai.

Wuri na farko da shugabar gwamnatin jamus zata fara sa kafa dai shine birnin parisa din kasar faransa ,batu dake nuni dacewa Merkel nada nufin dorewa da dangantakar kawance dake tsakabnin jamus da faransa na lokaci mai tsawo a matsayinsu na jagoran turai.

A gobe laraban Daga Faransa,shugabar gwamnatin Jamus Merkel zata ziyarci Brussels ,kana ranar alhamis ta wuce birnin london din Britania.

Wannan ziyara nata zuwa kasashen Britania da faransa a mataki na farko dai bazai kasa nasaba da zuwa neman shawarwarin shugaba Jacque Chirac da Tony Blair ,wadanda ke zama tsoffin hannaye cikin harkokin gwamnati,wanda zai bata daman sanin irin shirin da zatayi na halartan taron kungiyar gamayyar turai da zai gudana ranakkun 15 da 16 ga watan disamba,taron da zata halarta a karo na farko da hawanta kujeran shugabancin gwammnatin jamus.

Taron kungiyar ta Eu dai zai kasance dama na karshe na cimma yarjejeni kann kasafin kudin kungiyar na shekarata 2007-13,batu daya jima wakilan kungiyar na tababa akai.

A birtanian,anasaran Angela Merkel zata nemi alkawarin inganta huldodi tsakanin london da Berlin,sabanin yadda lamarin yake karkashin gwamnatin Gehard Schroder.

A yayinda a birnin Brussels a gobe anasaran Merkel zata gana shugaban hukumar gudanarwa na kungiyar gamayyar turai Jose Manuel Barroso,da shugaban majalisar turai Josep Borrell,da sakatare general na kungiyar NATO Jaap de Hoop Scheffer.

A sakonsa na taya murna,shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yabawa wannan zabe daya bawa Angela Merkel wannan mukami,inda yayi alkawarin inganta dangantaka na kut da kut tsakanin kasashen biyu.

A wata sanarwa daga Moscow bayan yan majalisar dokokin Bundustag na Jamus sun tabbatar da matsayin Merkel,Putin ya gayyaceta tuwa Rasha ,tare da tabbatar da dorewan dangantaka tsakanin Rasha da Jamus.