Halin kunci sakamakon haramta amfani da babura a Adamawa
August 26, 2015Bayan da mahukunta suka dauki wannan mataki saboda kalubalen tsaro a a jihar ta Adamawa, lamarin dai zai matukar shafar hanyoyin arzikin jama'a.
A tsakiyar watan Agusta ne rundunar sojin Najeriya da ke birnin Yola ta tabbatar da haramcin amfani da babura a fadin jihar Adamawa a wani kokari na yaki da 'yan kungiyar Boko Haram da ke amfani da babura wajen kai hare-hare da ma wasu zirga-zirgarsu a dazukan jihar.
Koken talakawa game da dokar
Sai dai tuni jama'ar da harkokinsu suka dogara kan baburan suka soma kokawa kan wannan mataki na soji musamman ma 'yan Acaba da kanikawa da ma wadansu da ke sayar da kayaki na baburan.
Baya ga wannan rukuni na jama'a dai su ma manoma da ke zama kaso mafi girma a baki dayan kayukan da ke a kananan hukumomin jihar ta Adamawa, na fama da radadi na wannan doka, saboda tasirin baburan ga ayyukansu.
Ko shakka babu wannan doka ta shafi harkokin tattalin arzikin jama'a da yawan gaske a jihar da ke daya daga jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya da ke fama da matsalolin rashin tsaro.