Hare-hare na illata sana'o'i a yankin tafkin Chadi
September 2, 2022Wadansu da ke da masaniya kan harin sun bayyana cewa ya yi matukar muni saboda yadda mayakan suka yanka yawancin masuntan na yankin tafkin Chadi tare da yin garkuwa da wasu da ba a san halin da su ke ciki ba. Tuni wasu mazauna tisbiran tafkin suka fara tserewa saboda gargadi da mayakan na Boko Haram suka yi musu na barin wajen ko kuma duk abun da ya same su suka jiyo.
An ruwaito cewa mayakan na Boko Haram na zargin masuntan da taimaka wa jami'an tsaro a yaki da ake yi da su, bayan da wasu matakai da jam'ian tsaro ke dauka suka fara yin tasiri a wannan yankin.Wannan hari wanda shi ne mafi muni tun lokacin da aka fara mayar da ‘yan gudun hijira zuwa garuruwansu, ya jefa sana'arsu cikin mawuyacin hali tare da tsayar da kusan dukkanin harkokin da ake yi na kamun kifi a gabar tafkin Chadi.
Maikano Sabo da ya tsira daga wannan hari, ya ce: "Mun shiga wani hali na Kaka-ni-ka-yi saboda wannan wuri da muke zuwa yanzu shi ne wajen neman abincinmu, kuma ga shi wurin an dakile shi...Ga mu nan mun taru ba mu san halin da muke ciki ba.”
'Yan Boko Haram na neman gurganta arzikin tafkin Chadi
Yawancin masuntan da aka halaka 'yan gudun hijira ne da suka koma garuruwansu domin ci gaba da rayuwa. Wannan ya sa masana da masharhanta kamar Lawali Ibrahim Babangida bayyana fargabar yadda rayuwar mutanen da suka koma garuruwansu za ta kasance musamman wadanda suka dogara da sana'o'i irin na kamun Kifi.
Ya ce: "Babban koma-baya ne kuma barazana ce ga mutanen wannan yankunan da abun ya fi shafa. Don kaha ana bukatar ganin an hada karfi da karfe wajen ganin cewa an tabbatar da irin wannn abu ya daina faruwa a cikin al'umma.”
A cewar Hafizu Aminu Daiba, wannan hari kan masunta wata makarkashiya ce ta kara dunkufar da harkokin tattalin arziki na Arewacin Najeriya. Ya ce: "Kiwo da noma ba za su iya yiwuwa ba, sai dan abin da ba za a rasa ba. Yanzu ga shi kamun kifin da ya saura wa ‘yan Arewa musamman mutanen kauyuka don samun dan abin da za su ci, shi ma an kassara shi.”
Masana na kira ga gwamnati da ta dauki karin matakai
Masharhanta na ganin cewa matukar gwamnatin Najeriya ba ta dauki mataki na bada kariya ga manoma da makiyaya gami da masunta da sauran masu sana'o'i a wannan yankin ba, da wuya a iya cimma nasarar mayar da mutane garuruwan kamar yadda hukumomi suka nufa.