1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Bam a zaben 'yan Majalisun Dokokin Pakistan

May 11, 2013

Hare haren bama bamai a birnin Karachi da wasu yankuna na Pakistan, ya kashe mutane 17, a yayin da al'ummar kasar ke kada kuri'unsu a zaben kasa baki daya.

https://p.dw.com/p/18W3Y
Pakistani volunteers carry injured blast victims to a hospital following a bomb explosion in Karachi on May 11, 2013. A Taliban bomb attack targeting an election candidate killed at least 11 people and wounded 36 others in Pakistan's financial hub of Karachi as polls got under way, a doctor said. The bomb targeted a candidate seeking election to the Sindh provincial assembly for the Awami National Party (ANP), the main secular party for ethnic Pashtuns, police said. AFP PHOTO / RIZWAN TABASSUM (Photo credit should read RIZWAN TABASSUM/AFP/Getty Images)
Hoto: RIZWAN TABASSUM/AFP/Getty Images

A wanna Asabar din ce al'ummar kasar Pakistan ke kada kuri'unsu domin zaben 'yan majalisar da zasu wakilce su. Wannan zaben dai shine zai kasance zakaran gwajin dafi, na sauyin mulki daga sojoji da suka mulki kasar na tsawon lokaci zuwa hannun farar hula. Wadanda suka cancanci zabe miliyan 86 ne dai ake saran za su kada kuri'un nasu a rumfunan zabe dubu 70 dake sassan kasar, domin zaben wakilai da zasu haye kujerun majalisar 272. To sai dai fargabar rigingimu na cigaba da yin dandazo ga zaben na Pakistan. Tuni dai aka dauki tsauraran matakan tsaro da jami'an 'yan sanda dana soji sama da dubu 600. Kusan mutane 130 ne dai kawo yanzu suka rasa rayukansu, a hare haren da aka kai gabanin zaben. Ko da safiyar yau sai aka samu tashin bama bamai a birnin Karaci, wanda ya kashe mutane 11 tare da raunata wasu masu yawa. Jam'iyyun tsohon Firaministan Nawaz Sheriff da ta fitattcen dan wasan motsa jiki na Pakistan Imran Khan ne dai ake hasashen zasu fafata wajen neman kujeru mafi rinjaye a Majalisar kasar.

Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Yahouza Sadissou Madobi